Luguden jiragen Sojojin sama ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram fiye da 70

Luguden jiragen Sojojin sama ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram fiye da 70

  • Dakarun Sojojin sama sun kai wa wasu ‘Yan ta’addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) hari
  • Jawabin da rundunar sojojin saman Najeriya ta fitar a jiya ya ce an hallaka ‘Yan ta’adda kimanin 70
  • Jiragen saman Najeriya da na Nijar sun kashe Sojojin ISWAP barkatai, wasu sun samu munanan rauni

Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta bada sanarwar hallaka wasu daga cikin mayakan kungiyar ISWAP da suka yi kaurin suna wajen ta’addanci.

Channels TV ta ce sanarwar da ta fito a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu 2022, ta tabbatar da cewa sojojin sama sun kashe dakaru fiye da 70 da ‘yan ta’addan.

An yi nasarar hallaka wadannan ‘yan ta’adda na Islamic State West Africa Province ne a yankin tafkin Chadi a kusa da iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Jawabin ya tabbatar da cewa jiragen Najeriya da na kasar Nijar su ka taimaka wajen kai harin.

Kamar yadda Punch ta bayyana, sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar sojojin sama na kasa watau Air Commodore Edward Gabkwet.

A irin wannan lokaci da ake sauraron saukowan ruwa, jami’an sojoji su kan yi kokari su kai yaki wajen ‘yan ta’addan domin a hana su samun mafaka a damina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiragen Sojojin sama
Wani jirgin saman Super Tucano Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“An kai hari a wurarern da ake zargi ‘yan ta’adda su ke …a ranar 13 ga watan Afrilu 2022 aka hangi ‘yan ta’adda a wani wuri da ake zargi sansaninsu ne.”
A dalilin haka, sai aka kai hari da jiragen saman Najeriya da na Jamhuriyyar Nijar a ranar 14 ga watan Afrilu a Tumbun Raho da wani sansanin koyon fada.

Kara karanta wannan

Sabon hari: An sheke dan bindiga yayin da gungunsu suka kai hari ofishin 'yan sanda

“Sama da ‘Yan ta’addan ISWAP 70 aka hallaka ko kuma aka yi masu mummunan rauni.”

- Edward Gabkwet

ISWAP sun addabi tafkin Chadi

Rahoton ya ce tun a shekarar 2016 ake fama da Islamic State West Africa Province (ISWAP) a yankin tafkin Chadi da suka fitina al’umma da sunan jihadi.

ISWAP da abokan fadansu na Boko Haram sun hallaka sama da mutane 40, 000 a Duniya. A halin yanzu akwai mutane miliyan biyu da dole sun bar gidajensu.

Yakin Rasha v Ukraine

A 'yan kwanakin nan aka fara samun rahotanni da ke nuna cewa Kasar Rasha ta na yi wa kasashen da ke makwabtaka da ita barazana da karfin nukiliya.

Rasha za ta yi amfani da makaman nukiliya idan Siwidin da Finland suka shiga NATO. Tun farko wannan ne dai ya jawo sabani tsakanin Rasha da kasar Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel