Kayanmata: Tsohon mijin Jaruma ya mata fallasa, yace kayanmatan bogi take siyarwa

Kayanmata: Tsohon mijin Jaruma ya mata fallasa, yace kayanmatan bogi take siyarwa

  • Tsohon mijin fitacciyar mai siyar da kayan mata, Jaruma, Fahad ya bayyana cewa yana kula ta ne kawai saboda dan shi da ke hannunta
  • Matashin ya bayyana cewa ya bar Jaruma duk da burga da dukan kirjin da take yi kan kayan matanta wadanda yace basu aikin komai
  • Fahad ya shawarci Jaruma da cewa ta daina yaudarar 'yan Najeriya da mabiyanta ta hanyar amfani da shi tana hada karairayi

Fitacciyar mai siyar da maganin mata, Jaruma, wacce ta kasance a kanun labarai kowanne mako,ta sha bajiya daga tsohon mijinta a kafar sada zumunta ta Instagram.

A wata wallafa da aka gani a Instagram, Fahad ya yi bayani kan cewa aurensa da Jaruma ya kare kuma shi ya fara barinta tare da yin watsi da lamarinta.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman kannywood maza 4 da suka shafe sama da shekaru 20 suna fim kuma ake yi da su har yau

Kayanmata: Tsohon mijin Jaruma ya mata fallasa, yace kayanmatan bogi take siyarwa
Kayanmata: Tsohon mijin Jaruma ya mata fallasa, yace kayanmatan bogi take siyarwa. Hoto daga @thetattleroomng/@jaruma
Asali: Instagram

Ya cigaba da cewa, yana tuntubar mai siyar da kayan matan ne saboda dan shi da ke hannunta kuma ya dace ta daina yaudarar mabiyanta.

Fahad ya kara da wallafa hoton sakon da ya tura wa tsohuwar matarsa domin samun su yi magana, amma yace ta wallafa domin neman nuna cewa yana bibiyarta.

Duba wallafar:

'Yan Najeriya sun yi martani kan wallafar Fahad

@whyte_le yace: "Hatta mabiyanta sai da suka samu nasu rabon."
@blesskidw ta ce: "Idan mai kayanmata za a bar ta, toh ni wace ce?"
@tracyikhille: "Amma yadda matar nan ta dade tana yaudarar miliyoyin mata tsawon shekaru kuma tana karbe kudadensu, ya dace a yi nazarinsa a makarantun kasuwaci."
@rity.01 cewa tayi: "Ahhhh... Yanzu yaya kwastomominta za su yi?"
@ironbarlyn: "Ta yuwu asirinta yana aiki ne kan mabiyanta kawai."

Kara karanta wannan

Fatima: 'Yar Kano, Mai Sana'ar Sanya 'Tile', Ta Zama Gwarzuwar Shekara A Taron Karrama Masu Sana'ar Hannu, Ta Lashe Lambobin Yabo Guda 3

Jaruma mai Kayan Mata ta cigaba da wallafa bidiyoyin Regina Daniels, duk da uwar-watsin da aka yi a kotu

A wani labari na daban, fitacciyar ƴar Najeriyar wacce tayi suna a kafar sada zumuntar zamanin nan wurin siyar da kayan mata, Hauwa Saidu wacce aka fi sani da Jaruma, ta ci gaba da wallafa bidiyoyin jarumar Nollywood, Regina Daniels.

Yayin magana da masu amfani da yanar gizo, mai saida kayan matan ta cigaba da ɗora wallafar Regina Daniels a shafinta, duk da irin badaƙalar dake tsakanin su.

Jaruma ta wallafa bidiyonta da Regina a asibiti, lokacin da bata da lafiya inda take bata magani. Mai saida maganin matan ta cigaba da tallata hajarta mai bunkasa jindadi ga maaurata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng