Gwamnan APC ya saki bidiyo yana cashewa a yayin da ake tsaka da rade-radin mutuwarsa

Gwamnan APC ya saki bidiyo yana cashewa a yayin da ake tsaka da rade-radin mutuwarsa

  • Matar gwamnan jihar Ondo ta yi watsi da jita-jitan da ake ta yadawa na mutuwar mijinta a wani asibitin kasar waje
  • A wata wallafa da ta yi a shafinta na Facebook, Betty Anyanwu-Akeredolu ta yi ba a ga masu yiwa mai gidan nata fatan mutuwa
  • A cikin bidiyon da ta saki, an gano mijin nata yana wakokin tare da cashewa shi da wani hadiminsa

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da na kewaye da shi sun yi martani a kan rade-radin mutuwarsa.

A kwanan nan ne wasu rahotannin kafofin watsa labarai suka yi ikirarin cewa gwamnan na nan an bashi gado a wani asibitin kasar waje.

Gwamnan APC ya saki bidiyo yana cashewa a yayin da ake tsaka da rade-radin mutuwarsa
Gwamnan APC ya saki bidiyo yana cashewa a yayin da ake tsaka da rade-radin mutuwarsa Hoto: Rotimi Akeredolu

Sai dai kuma babban sakataren labaransa, Mista Richard Olatunde, a wani jawabi da ya saki, ya soki rahoton, yana mai cewa Akeredolu ya aika wata wasika majalisar jihar a ranar 23 ga watan Maris, 2022, cewa zai tafi hutun aiki na kwanaki 14 sannan ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

A makon da ya gabata, wani rahoto ya sake ikirarin cewa gwamnan ya mutu a wani asibitin kasar Jamus.

Matar gwamnan, Misis Betty Anyanwu-Akeredolu, wacce ta wallafa wani bidiyo da tuni ya karade yanar gizo a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewar mijinta na hutu a yanzu haka.

A wani bidiyo mai tsawon sakwan 19, an gano gwamnan a cikin wani daki tare da wani mutum da ake zaton daya daga cikin hadimansa ne suna wakar yabo da rawa. Ba a bayyana ranar da aka dauki bidiyon ba.

Matar gwamnan ta rubuta:

“Baba Aketi kenan! ka ci gaba da jin dadin hutunka. Me nake ji? Kune za ku shiga wutar jahannama."

Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ritaya kanal Bala Mande, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan gama wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Mande ya bayyana cewa sun zauna sannan sun yanke shawara kan batun sauya shekar Yari da Marafa sannan sun cimma yarjejeniyar aiki don ci gaban jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng