Limaman cocin Katolika da Anglika sun bukaci Buhari da yayi murabus
- Manyan limaman majami'un Anglika da Katolika da ke Kaduna sun goyi bayan dattawan arewa kan bukatar murabus din Buhari
- A cewar Bishop Timothy Yahaya da Mathew Manoso Ndagoso, in har shugaba ya gaza kare rayuka, kamata yayi ya sauka daga kujerarsa
- Sun caccaki wadanda ke baibaye da shugaban kasan tare da tabbatar da cewa tarihi ba zai manta da barnar da gwamnatinsa ta yi ba
Kaduna - Babban limamin Anglican Communion, Timothy Yahaya da babban limamin Catholic Archdiocese, Matthew Manoso Ndagoso, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus kan tsanantar rashin tsaro a kasar nan.
Vanguard ta ruwaito cewa, wannan kiran na kunshe a sakonnin bikin Easter da suka fitar inda Bishop Yahaya yace abinda ya fi dacewa shugaba yayi idan ya gaza shi ne ya sauka daga kujerarsa.
2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasa Ta Ranar Talata, Ministan Buhari
Hakazalika, Bishop Ndagoso ya ce akwai wuya mutum yace zai ki aminta da matsayar dattawan arewa da suka ce akwai bukatar Buhari yayi murabus daga kujerarsa kan kashe-kashen da suka ki ci balle cinyewa a kasar nan.
Ya ce abinda mutane a kodayaushe suke samu shine kisa, sata da garkuwa da su tare da alkawarin bogi da shugabannin ke cigaba da yi na cewa zasu samar da tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sakon Easter na shine ina son sanar da kowanne dan Najeriya cewa, Najeriya na da rabo a matsayinta na kasa. Na san me muke fuskanta, akwai matukar hatsari kuma wannan lokacin wahala ne. Amma ina tabbatar muku akwai gobe."
A rahoton jaridar Punch, ya kara da cewa:
"Bana son hada lamurra da dattawan arewa saboda ni ba dan siyasa bane. Amma a gaskiya game da shugabanci akwai da'a. Idan ba za ka iya sauke nauyin da ke kanka ba, abinda yafi dacewa shi ne ka yi murabus.
"Amma abinda yafi daga min hankali shi ne bani da tabbacin idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san sunanshi nitsewa yake a tarihi a matsayin shugaban kasan da ke kallo ana kashe mutanensa.
"Duk da shi ne ministan man fetur. A yau a Kaduna bamu da fetur na tsawon watanni. A matsayinsa na shugaban kasa wanda kasa ke hannunsa, ASUU sun rufe jami'o'i, don haka makomar mu ba za ta yi kyau ba."
Ya kara da cewa:
"A matsayin sa na shugaban kasa wanda ke duba lamurra da yawa inda za ka ji an yi kasafin biliyoyin naira amma ba mu ganin komai da aka yi da su.
"Toh ni ba a matsayin dan siyasa nake magana ba, ina magana ne a matsayin dan kasa, ina magana ne da muryoyin talakawa, ina magana ne da abinda nake gani."
"Ban sani ba, wadanda ke baibaye da shugaban kasa, kuna son ku cire sunansa daga albarkar gobe ne? Ina fatan kun san bai dace abinda kuke yi ba idan kuna hana shi jin bayanai game da kasar."
Dattawan Arewa sun bukaci murabus din Buhari, sun sanar da dalilinsu
A wani labari na daban, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta bukaci murabus din shugaban kasa Muhammadu Buhari nan take sakamakon yawaitar kashe-kashe a fadin kasar nan ballantana arewaci.
Daily Trust ta ruwaito cewa, daraktan yada labaran kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi wannan kiran a ranar Talata.
"Mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari bai magance kalubalen tsaro da muke ciki ba. Ba za mu cigaba da rayuwa tare da mutuwa a karkashin makasa, masu garkuwa da mutane, masu fyade da sauran kungiyoyin ta'addanci da suke hana mu hakkinmu na zaman lafiya da tsaro ba."
Asali: Legit.ng