Zamfara: Dan bindiga Nasanda ya ba Matawalle kwana 14 ya biya shi N30m, ko ya halaka rayuka 300
- Fitaccen shugaban 'yan bindiga a jihar Zamfara, Nasanda, ya bai wa gwamnatin jihar wa'adin kwana 14 da ta biya shi N30m
- A cewar Nasanda, 'yan sa kai sun halaka amaryarsa, kawunta da innarta, fansar rayukansu kuwa ran mutum 300 idan ba a biya shi N30m ba
- Nasanda ya jaddada cewa za su kai hari in har ba a biya diyyar ba, kuma ba za su bar jama'a su zauna lafiya ba idan ba a shafa wa Fulani lafiya ba
Zamfara - Nasanda, wani shahararren mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara ya bai gwamnatin jihar wa'adin kwana 14 da ta biya shi N30 miliyan a matsayin diyyar matarsa da 'yan uwanta biyu.
Ya yi barazanar kashe rayuka 300 idan har ba a cika masa bukatarsa ba, Vanguard ta ruwaito.
Nasanda ya yi ikirarin cewa amaryarsa, kawunta da innarta duk 'yan sa kai ne suka halaka su a jihar.
HumAngle ta ruwaito cewa, a wani sautin murya da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Nasanda ya ce da gangan aka kashe masa amaryarsa, kawunta da innarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya zargi cewa 'yan sa kan sun san cewa suna da alaka da shi. A sautin muryan, ya ce ya yi matukar adalci kuma bai nuna son kansa ba da ya bukaci N30 miliyan a matsayin diyya.
"Idan da ni mai son kaina ne, zan bukaci N50 miliyan ne a kan kowanne mutum daya," yace.
Kamar yadda yace, "Ba zan bada wa'adin watanni ba, kwanaki 14 na bada kuma a cika bukata ta. Kuma ba za mu kai farmaki ba sai jama'a suna gonakinsu. Idan ba a kyale Fulani sun yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali ba, mu ma ba za mu bar jama'a su zauna lafiya ba," yace.
"Idan gwamnatin ta kasa biyan kudin, zan yi abinda na saba. Ina nufin zan halaka rayukan mutum 300 domin daukar fansar mutuwar amaryata da 'yan uwanta biyu. Tabbas, rayukan mutum 300 za su kasance cikin hatsari," yace a sakon muryar da ya saki.
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe
A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kutsa wani yanki na garin Tsafe kuma sun sace dalibai biyar na kwalejin kiwon lafiya da fasaha da ke tsafe a jihar Zamfara.
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Laraba. Wata majiya ta sanar da cewa miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai ne suka dira gidan daliban wanda yake wajen makaranta.
Asali: Legit.ng