2023: Kwamishinan Ganduje yayi murabus, yana son gaje kujerar gwamnan Kano
- Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi murabus daga mukaminsa
- Wannan na zuwa kasa da sa'o'i 24 da Gwamna Abdullah Ganduje ya bada sanarwar cewa duk mai son yin takar ya yi murabus daga mukaminsa
- Wannan sanarwar ta Gwamna Ganduje tana biyayya ne ga sashi na 84, sakin layi na 12 na gyararrun dokokin zabe
Kano - Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Musa Kwankwaso, ya yi murabus, jaridar Punch ta ruwaito.
Murabus dinsa ya zo ne sa'o'i kadan bayan Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bai wa masu mukaman siyasa wa'adin sa'o'i 24 su yi murabus in har za su fito takara.
A wani sautin murya da ya fitar, Kwankwaso ya mika godiya ga Ganduje kan damar da ya bashi na hidimtawa jihar.
Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari
Idan za a tuna, Ganduje ya fitar da wata takarda a ranar Lahadi inda ya umarci dukkan masu mukaman siyasa da ke son fitowa takara da su yi murabus a mutunce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan umarnin yana biyayya ne ga tanadin sashi na 84 sakin layi na 12 na sabuwar gyararriyar dokar zabe, jaridar Solacebase ta ruwaito.
Kwamishinan ruwa na jihar Kano, Sadiq Wali, tun farko ya yi murabus inda ya saiya fom din takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Gwamna Ganduje ya ba mukarrabansa daga nan zuwa gobe Litinin su ajiye mukamansu
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.
A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurci dukkanin masu rike da mukaman siyasa da ke son yin takarar kujeru a zaben 2023 mai zuwa da su yi murabus daga mukamansu.”
Daily Post ta rahoto cewa wasu kwamishinoni, hadimai da ma sakataren gwamnatin jihar na neman takarar mukamai daban-daban na gwamnati.
Tun farko dai kwamishinan Ganduje kan albarkatun ruwa, Sadiq Wali, ya yi murabus daga kujerarsa sannan ya yanki fom din takarar gwamna a karkashin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP.
Asali: Legit.ng