'Yan sanda sun yi ram da dillalin kwayoyi a Kano dauke da sinki 250 na wiwi masu darajar N1.7m
- Rundunar 'yan sanda jihar Kano tayi ram da wani mai dillalin wiwi a iyakar dake tsakanin jihar Kaduna da Kano, bayan ya yi yunkurin shiga Kano da wiwi
- Kakakin rundunar ya bayyana yadda aka kama wani Agbo Victor dan jihar Edo wanda ya yi kokarin aukawa Kano da sunkin wiwi 250 masu kimar N1.7m da nufin kaima wani Alhaji
- Alhajin ya ranta a na kare bayan yaji labarin kama abokin harkallarsa, yayin da ake cigaba da bincike kuma za a gurfanar dashi gaban kotun da zarar an kammala
Kano - Jami'an tsaron rundunar'yan sandan jihar Kano sun yi ram da mai safarar miyagun kwayoyi, inda suka samu sunkin wiwi 250 masu darajar N1.7 miliyan, The Nation ta ruwaito.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Juma'a, 15 ga watan Afirilu, ya ce wanda ake zargin Agbo Victor, ya bada labarin yadda ya yi safarar miyagun kwayoyi daga jihar Edo zuwa Kano.
"A ranar 20 ga watan Maris, 2022, misalin karfe 4:00 na safe, wata tawagar dake yaki da amfani da miyagun kwayoyi karkashin jagorancin CSP Hassan Nasir Jega, mai kula da babban titin Kano, yayin sintiri wurin Kwanar Dangora na karamar hukumar Kiru dake tsakanin iyakar Kaduna da Kano.
"Sun kama wani Agbo Victor, mutum mai shekaru 33 na jihar Edo, yana tuka motar Honda Hennessy kalar koriya mai duhu, dauke da bandiran wasu ganyayyaki guda 250 wanda ake zargin wiwi ne, masu kimar Naira miliyan daya da dubu dari bakwai da hamsin (1,750,000.00) a cikin but din motar," a cewar kakakin.
Yayin bincike, wanda ake zargin ya bayyana cewa kayayyakin da ke cikin but din motar sinkin wiwi ne guda 250, sannan ya dauko su daga jihar Edo zuwa jihar Kano da niyyar kaiwa wani Alhaji, inda aka yi ram dashi a iyakar Kaduna da Kano.
LIB ta ruwaito cewa, bayan gano an kamashi, Alhajin ya tsere zuwa wani guri da ba'asani ba.
Sai dai ba tare da jinkiri ba, kwamishinan 'yan sanda ya ce a mika lamarin ga hukumar binciken sirrin na 'yan sandan, sashin binciken miyagun kwayoyi. Da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
CP ya yi matukar jan kunnen ce hatsabibai ba za su samu maboya ba a jihar Kano ba, sannan ya shawarcesu da su tuba ko su bar jihar gaba daya.
NDLEA ta kama sinkin hodar iblis 101 a cikin bargunan yara a Legas
A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu sunki 101 na hodar Iblis da aka boye a bargon yara a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, wanda ya tabbatar da kamen ta wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a shafin hukumar na Twitter, ya ce miyagun kwayoyin sun samu shigowa kasar nan ta hanyar wani dattjo mai shekaru 52 da ke dawowa daga kasar Brazil.
Wanda aka kama da miyagun kwayoyin mai suna Akudirinwa Hilary Uchenna, dan asalin karamar hukumar Oru ta gabas ne da ke jhar Imo.
Asali: Legit.ng