Saudiyya ta nemi limamai su daina tsawaita addu'ar Al-kunutu a yayin sallolin tahajjud

Saudiyya ta nemi limamai su daina tsawaita addu'ar Al-kunutu a yayin sallolin tahajjud

  • Hukumomi a kasar Saudiyya sun bukaci limaman da ke jagoranci a sallolin tahajjud da su daina tsawaita addo'in Alkunutu a goman karshe na Ramadana
  • Ma'aikatar harkokin addini ta kasar ta nemi a dunga kammala sallar kafin kiran sallar asubahi domin mutane su samu isasshen lokaci tsakanin sallolin biyu
  • Ta kuma bukaci limamai da su zamo masu kankan da kai da tawali'u yayin addu'a sannan su guji zuzuta murya da kuma rera ta

Saudiyya - Ma’aikatar harkokin addini ta kasar Saudiyya ta ja hankalin limaman da ke jan sallolin tahajjud a goman karshe na watan Ramada a masallatan kasar da su dunga takaita addu’o’in Al-kunutu domin saukakawa masu binsu sallah

Kamar yadda Saudi Gazette ta rahoto, ma’aikatar ta bukaci limaman da su dunga kammala sallar da wuri kafin kiran sallar Asubahi da dan takaitaccen hutu a tsakani domin kada masallata su ji gajiya.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Saudiyya ta nemi limamai su daina tsawaita addu'ar Al-kunutu a yayin sallolin tahajjud
Saudiyya ta nemi limamai su daina tsawaita addu'ar Al-kunutu a yayin sallolin tahajjud Hoto: Saudi Gazette
Asali: UGC

Har ila yau, ma’aikatar ta bukaci limaman da su yi aiki da koyarwar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da Alkunutu da sauran addu’o’in da aka rawaito yana yi.

Rahoton ya kuma kawo cewa ma'aikatar ta yi kira ga limaman da su guji tsawaita addu’o’i da mayar da su huduba. Sannan su daina zuzuta muryoyinsu da rera ta, maimakon haka su yi addu'a cikin kankan da kai da tawali'u.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka kuma, ma’aikatar ta bukaci jama’a da su kara yiwa shugabannin kasashensu da sojojin da aka tura domin kare iyakokin kasashen addu’a a ranakun da suka yi saura na Ramadana.

Dole malamai su dunga fadar gaskiya kan halin da Najeriya ke ciki – Sheikh Khalid

A wani labafri na daban, Shugaban gidauniyar bincike da Da’awar Musulunci, Sheikh Nuru Khalid, ya ce limamai kadan ne ke da kwarin guiwar yin magana a kan mawuyacin halin da kasar ke ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Daily Trust ta rahoto cewa Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a wani shirin Trust TV na ‘Daily Politics’a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu.

An dakatar da Sheikh Khalid, wanda ya kasance babban limamin masallacin Apo da ke Abuja, sannan daga baya kwamitin masallacin ya sallame shi gaba daya saboda ya soki gwamnatin Buhari a hudubarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel