NBS: Tsadar biredi, gas da mai sun jawo tashin farashin sauran kayayyaki a Najeriya
- Mummunan yanayin tattalin arziki na kara tasiri mai yawa kan kusan dukkanin kayayyaki a kasuwa a fadin Najeriya
- Wannan na zuwa ne kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta yi bayani dalla-dalla kan kayayyakin da suka haifar da hauhawar farashin sauran kayayyakin a kasar a watan Maris
- Bisa kididdigar da aka yi, an gano cewa hauhawar farashin biredi, man fetur, iskar gas da sauran manyan kayayyaki sun yi tasiri sosai ga tattalin arzikin kasar
Yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu da 15.92% A cikin watan Maris din 2022, kamar yadda wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ya nuna.
The Cacble ta tattaro cewa, rahoton ya bayyana cewa an samu kari a farashin iskar gas, biredi, hatsi, mai da sauran kayayyakin abinci.
Ya ce ma'aunin farashi na masu sayen kayayyaki na CPI nawata-wata ya karu da maki 0.22 daga 15.70% da aka gani a watan Fabrairu.
Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC
Sai dai, bisa ga ma'aunin shekara-shekara, farashin ya ragu daga 18.17% cikin dari da aka gani a cikin watan Maris din 2021, inji rahoton Daily Trust.
A cewar rahoton:
"Wannan yana nufin cewa hauhawar farashin kaya ya ragu a cikin Maris 2022 idan aka kwatanta da watan Maris na shekarar da ta gabata."
Rahoton ya ce hauhawar farashin kayayyaki a birane ya karu zuwa 16.44% a duk shekara a watan Maris na 2022, wanda ke nuna raguwar maki 2.32 cikin dari daga adadin da aka samu a watan Maris na 2021 (18.76%).
Kayayyakin karkara
Kididdigar farashin kayayyakin karkara ya tashi zuwa 1.73% a cikin Maris 2022, tare da karuwar maki 0.12 daga 1.61% da aka gani a watan Fabrairun 2022.
Hakanan, a bangaren abinci, an samu karuwa zuwa 17.20% a cikin Maris 2022 idan aka kwatanta da 22.95% da aka gani a cikin Maris 2021.
Rahoton ya yi karin haske da cewa:
"Wannan tashin da aka samu a kididdigar kayan abinci ya faru ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, kayayyakin abinci kamar, dankali, dawa da sauran kayan saiwa, kifi, nama, mai da kitse."
Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari
A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta yiwa yan Najeriya a shekarar 2015 a dukkan bangarori, musamman gidaje.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin kaddamar da gidaje 68 da ma'aikatar gidaje da ayyuka ta gina a titin Benin-Auchi, jihar Edo. Buhari wanda ya samu wakilcin ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, yace:
"Lokacin da jam'iyyarmu All Progressives Congress (APC), ta bukaci goyon bayanku a 2015, mun yi alkawarin zaku ga canji. Wannan rukunin gidajen misalin ne cika alkawarin da muka yi."
Asali: Legit.ng