Cikin Ramadan: Jami'an tsaron Isra'ila sun farmaki Musulmai a masallacin Qudus

Cikin Ramadan: Jami'an tsaron Isra'ila sun farmaki Musulmai a masallacin Qudus

  • Rahoton da muke samu daga kasashen ketare na nuni da cewa, da sanyin safiyar yau Juma'a ne jami'an tsaron Isra'ila suka farmaki Falasdinawa a Qudus
  • Wannan lamari bai yi dadi ba, domin kuwa ya kai ga harbin mai gadin masallacin a ido da harsashin roba
  • Hakazalika, rahotanni sun bayyana cewa, akalla mutane 117 ne daga cikin Falasdinawa suka jikkata sakamakon harin

Falasdinu - Wani rahoton jaridar Arab News ya ce, jami'an tsaron Isra'ila sun shiga harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus da asuba ranar Juma'a a daidai lokacin da dubban Falasdinawa suka taru domin gudanar da sallah a cikin watan Ramadan.

Lamarin dai ya haifar da artabu, inda ma'aikatan lafiya suka ce akalla Falasdinawa 117 ne suka jikkata.

Isra'ila ta ce dakarunta sun shiga masallacin ne domin kwashe wasu duwatsu da aka tara da nufin tada hankali, inji rahoton GulfNews.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Farmakin 'yan Isra'ila kan Musulmai
Cikin Ramadan: Dakarun Isra'ila sun kai farmaki kan Musulmai a masallacin Qudus | Hoto: arabnews.com
Asali: UGC

Masallacin Al-Aqsa mai tsarki ya kasance cibiyar tarzoma tsakanin Isra'ila da Falasdinu, kuma an sha samun tashe-tashen hankula a lokuta masu tsawo.

Rikici a wurin a bara ya haifar da yakin kwanaki 11 da mayakan Hamas a zirin Gaza.

Rikicin ya zo ne a wani lokaci na musamman; Ramadan na wannan shekara ya zo daidai da Idin Ketarawa na Passover, babban hutun Yahudawa na mako guda da ke farawa ranar Juma'a da faduwar rana, da kuma mako mai tsarki na Kirista, Easter.

Ana sa ran bukukuwan za su kawo dubun-dubatar jama'a zuwa cikin Tsohon Birnin Kudus, gida ga manyan wuraren masu tsarki ga dukan addinai uku.

Bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaron Isra'ila ke cin zarafin Musulmai

Wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuna yadda Falasdinawan ke jifa da duwatsu, yayin da 'yan sanda ke harba barkwanon tsohuwa a kan jama'ar da ke kewaye da masallacin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta amince Buhari ya kashe $1bn domin shigo da wasu jiragen yaki

Wasu bidiyon kuma sun nuna yadda masu ibada ke kare kansu a cikin masallacin yayin da hayakin barkwanon tsohuwa ya turnuke masallacin.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce ta yi jinyar mutane 117 sakamakon farmakin na jami'an tsaron Isra'ila.

Red Crescent ta ce da dama daga cikin Falasdinawa sun samu raunuka daga harsashin roba, barkwanon tsohuwa da kuma dukan su da sanduna. Hukumar agajin ta ce an harbe daya daga cikin masu gadin wurin da harsashin roba a ido.

Ga wasu daga cikin bidiyon:

Wasu barayi sun sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya

A wani labarin daban, wasu gungun barayi sun tafka sata da tsakar rana inda suka yi awon gaba da gadar karfe mai tsayin mita 18.3 kan rafin Ara-Sone, garin Rohtas a gabashin kasar Indiya.

Kaakin Hafsan yan sanda, Subhash Kumar, wanda ya tabbatar da hakan ga AFP ya bayyana cewa barajin sun yi basaja ne da kayan ma'aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

Yace: "Sun dauke gadar cikin wata babbar mota."

A cewar yan garin Rohtas, barayin sun kwashe kwanaki uku suna kokarin sace gadar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.