Bidiyon yadda yan bindiga suka farmaki wurin Rijistar zaɓe, suƙa halaka Jami'in INEC

Bidiyon yadda yan bindiga suka farmaki wurin Rijistar zaɓe, suƙa halaka Jami'in INEC

  • Yan bindiga sun kai hari runfar zaɓen da hukumar INEC ke cigaba da yi wa mutane Rijistar zaɓe a shirin tunkarar 2023
  • Wani bidiyo ya nuna yadda yan ta'adda suka ci karen su babu babbaka a yayin harin, suka kashe ma'aikaci ɗaya
  • Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafara, IPOB, ce ake zargi da kai hare-hare kudu maso gabas, zargin da ta musanta

Imo - Wani ma'aikacin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ya rasa rayuwarsa lokacin da yan bindiga suka farmaki runfar zaɓe inda suke aikin rijista ga masu kaɗa kuri'a.

Lamarin ya faru a yakin ƙaramar hukumar Ihitte Uboma ta jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya.

Kakakin INEC na ƙasa, Festus Okoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata Sanarwa, ya bayyana sunan wanda ya mutu da Anthony Nwokorie.

Kara karanta wannan

'Kun yi a banza' Google ta aike da kakkausan sako ga mawallafa game da yaƙin Rasha da Ukraine

Daɗin daɗawa ya ce sauran mutum biyu dake aiki da Mamacin a Runfar zaben, har yanzun babu labarin inda suke bayan harin.

Yan bindigan da suka kashe ma'aikacin INEC.
Bidiyon yadda yan bindiga suka farmaki wurin Rijistar zaɓe, suƙa halaka Jami'in INEC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto cewa hukumar INEC ta dakatar da aikin yi wa mutane Rijistar zaɓe a yankin ƙaramar hukumar bayan harin.

A wani Bidiyo da ya watsu da dandalin sada zumunta na Whatsapp da kuma Twitter ya nuna yadda yan bindiga suka farmaki ma'aikatan da kuma mutanen da suka hallara domin yin rijista a wurin.

A cikin bidiyon, yan ta'addan sun umarci ma'aikatan su kwanta a ƙasa, suka cigaba da harbi ba tare da la'akari ba. An jiyo wani sauti suna gargaɗin cewa ba za'a yi rijistar INEC a yankin ba.

"Duba dan Allah, wai mutanen da muke yaƙi domin kwato musu yancin su, amma su kuma suna shirya wa zaɓe," Muryar ɗaya daga cikin yan bindigan ta faɗa yana mai nuna ma'aikatan da mazauna yankin, waɗan da mafi yawa Ibo ne.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya ɗaukar wa Yan Najeriya alkawari biyu idan ya zama shugaban ƙasa

"Yau 14 ga watan Afrilu, muna ƙara gargaɗin ku, ba mu son wani zaɓe. Ba maganar zaɓe kuma ba Katin Zaɓe, shin kuna tunanin muna wasa ne?" Ya jefa tambaya ga mutanen da ke wurin yana ɗauke da bindiga.

Yayin da yake magana, wasu yan bindiga biyu suka buɗe wuta kan wani mutum dake kwance ƙasa, wanda ake tsammanin ma'aikacin INEC ne da aka tabbatar ya mutu.

A bidiyon mai tsawon minti ɗaya da daƙiƙa 51, an ga mutum 13 a kwance ƙasa cikin su har da ƙaramin yaro a harin.

Kallo Bidiyon a nan

Maharan sanye da abun ɓoye Fuska, sun ɗauki kayayyakin INEC kuma suka lalata su. Sun farfasa na'ura mai kwakwalwa suka zubar a ƙasa, abubuwan zaman wurin duk ba su bar su haka nan ba.

Ƙungiyar yan aware IPOB ake zargin tana da alaƙa da hare-haren da ake kaiwa kudu maso gabas, amma ta musanta zargin. IPOB ta yi ƙaurin suna wajen fafutukar ɓallewa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe Fitaccen ɗan kasuwa har Lahira a gaban Budurwar da zai Aura mako mai zuwa

A wani labarin kuma Wutar Lantarki Ta Lantarke Wani Saurayi Har Lahira Yana Tsaka da Chajin Wayarsa iPhone

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai tattauna da shugabannin hukumomin tsaron ƙasar nan ranar Talata mai zuwa.

A ranar Alhamis da muke ci, Shugaban ya gana da majalisar magabatan ƙasar nan da ta ƙunshi shuwagabannin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262