Gwamna Yahaya Bello ya tsige daya daga cikin kwamishinoninsa
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya sauke kwamishinan lafiya na jihar, Dr Saka Haruna Audu, daga kan kujerarsa
- An tattaro cewa gwamnan ya dauki matakin ne kan zarginsa da wawure wasu makudan kudade
- Rahoton ya kuma bayyana cewa dakatarwar da gwamnan ya yi ma kwamishinan ya fara aiki a nan take
Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya sauke Dr Saka Haruna Audu daga mukaminsa na kwamishinan lafiya na jihar kuma matakin ya fara aiki nan take.
A cewar majiyoyi, an tsige kwamishinan ne kan zargin karkatar da wasu kudade, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wata majiya ta ce Dr Saka ya tattara kayansa daga ofishinsa da ke ma’aikatar lafiya ta jihar da ke garin Lokoja, babbar birnin jihar a ranar Talata.
An tattaro cewa wasu mutane na ta rokon gwamnan kan cewa kada ya bayyana lamarin ga duniya ta sani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kuma rahoto cewa Dr Saka ya sanar da wasu takwarorinsa cewa an dakatar da shi ne, amma ba a kore shi ba.
Daily Trust ta rahoto cewa duk wani kokari da aka yi domin jin ta bakinsa ya ci tura don ya ki amsa kiran waya da sakon waya.
Dr Saka na daya daga cikin kwamishinonin farko da Bello ya nada tun a wa’adin mulkinsa na farko.
Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan
A wani labari na daban, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng