Yanzu-Yanzu: An Bindige Ma'aikacin INEC Har Lahira A Wurin Yi Wa Mutane Rajistan Zabe

Yanzu-Yanzu: An Bindige Ma'aikacin INEC Har Lahira A Wurin Yi Wa Mutane Rajistan Zabe

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka jami'in hukumar INEC mai suna Nwokorie Anthony a Jihar Imo
  • Sakamakon halaka Mr Anthony, Hukumar INEC ta dakatar da cigaba da aikin yi wa mutane rajistan zabe a karamar hukumar Uboma a Imo inda abin ya faru
  • Festus Okoye, Kwamishina a hukumar INEC kuma shugaban kwamitin watsa labarai ne ya bada sanarwa, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki su samarwa ma'aikatan IEC tsaro

Jihar Imo - Yan bindiga sun halaka wani jami'in Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa, INEC, mai suna Mr Nwokorie Anthony a Jihar Imo.

Daily Trust ta rahoto cewa an bindiga jami'in ne yayin aikin cigaba da yi wa mutane rajistan katin zabe a karamar hukumar Uboma ta jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci

Yanzu-Yanzu: An Bindige Ma'aikacin INEC Har Lahira A Wurin Yi Wa Mutane Rajistan Zabe
An Bindige Ma'aikacin INEC Har Lahira A Imo. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

A cewar baturen zaben jihar, Farfesa Emeka Ezeonu, an kashe Nwokorie ne a Nkwo Ihitte (PU 004) a mazabar Amakohia (RA 02) a karamar hukumar Ihitte Uboma.

An dakatar da aikin yi wa masu zabe rajista saboda kisar Anthony, Okoye

Jaridar The Punch ta rahoto cewa saboda wannan abin bakin cikin, hukumar zaben ta dakatar da aikin yi wa mutane rajista a karamar hukumar.

Kwamishina a hukumar INEC kuma shugaban kwamitin watsa labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar, Festus Okoye, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

"Kafin afkuwar lamarin, hukumar ta dakatar da cigaba da rajistan masu zabe a kananan hukumomin Orsu da Njaba saboda rashin tsaro yayin da ake cigaba da rajistan a ofishin INEC na kananan hukumomin Oru East, Oru West, Orlu da Ohaji-Egbema."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

INEC ta mika ta'aziyya ga iyalan mammacin

Hukumar ta INEC ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan Nwokorie Anthony tana mai addu'an Allah ya gafarta masa ya kuma ba su hakurin jure rashinsa.

Okorie ya bukaci shugabanni a garuruwa da kungiyoyi a jihar Imo da masu ruwa da tsaki su bawa ma'aikatan INEC kariya domin su samu ikon sauke nauyin da kasa ta dora musu.

Ya ce:

"Tsaro da kiyayye lafiyar ma'aikatan hukumar mu abu ne mai muhimmanci, musamman yanzu da aka bawa kananan hukumomi da jihohi daman yin rajista."

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164