Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci
- An kama wasu matasa biyu a unguwar Tudun wadan jihar Kaduna da ake tuhumarsu da laifin yin 'ba haya' cikin Masallaci
- Kotun Shari'ah a jihar Kaduna ta bada umurnin garkame matasa biyu gidan gyara hali
- Abin da ya fara kaman wasa tsakanin matasan ya zama babban fitina cikin al'umma
Kaduna - Wata kotun Shari'ah dake Magajin Gari, Tudun Wada, jihar Kaduna ta bada umurnin garkame matasa biyu gidan gyara hali kan tuhumar yin 'ba haya' cikin Masallaci.
Yan sanda sun gurfanar da Matasan biyu - Nura Usman da Adamu Dauda - kan laifin tayar da tarzoma da kazanta cikin jama'a.
Alkali Rilwani Kyaudai, ya dage zaman zuwa ranar 28 ga Afrilu don yan sanda su gabatar da shaidu, rahoton Daily Nigerian.
Lauyan yan sanda, Ibrahim Shuaibu, ya ce mutan unguwa ne suka dankawa yan sanda Usman da Dauda ranar 11 ga Afrilu, 2022.
Ya ce an damke Usman yana 'ba haya' cikin Masallacin dake Alkalawa Road, Tundun Wada Kaduna misalin karfe biyu na rana.
Yace Dauda ya yi alkawarin baiwa Usman N20,000 idan yayi kashi cikin dakin bauta, shi kuwa yayi.
Kano: Kotun Shari'a Ta Bada Umurnin a Tsare Wani Saboda Ɗunkulen 'Maggi' Katon 22
A wani labarin, wata kotun sharia da ke zamanta a Kano, a ranar Talata, ta tsare wani mutum mai shekara 37, Yusha'u Ado, bisa zargins da satar sinadarin dandano na abinci katon 22.
The Punch ta rahoto cewa Ado wanda yan sanda suka gurfanar da shi bisa laifin 'kutse da cin amana da cuta', ya amsa laifin da ake tuhumansa.
Dan sanda mai gabatar da kara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotu cewa, wanda ya shigar da karar, Jamilu Ibrahim, mazaunin Galadanci Quaters, Kano, ya yi korafi kan abin a ofishin Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.
A cewar bayanan da yan sandan suka bada da farko, wanda ya yi karar ya kai korafi cewa ya bawa wani Ado ajiyar katon din sinadarin dandano katon 260.
Asali: Legit.ng