Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai

Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai

  • A ranar Alhamis ne majalisa ta amince da kashe Naira Tiriliyan 4 a tallafin man fetur kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bukata
  • A baya dai shugaba Buhari ya aike da bukata ga ‘yan majalisar tarayya a wani bangare na sake fasalin kasafin kudin 2021
  • A halin da ake ciki, Buhari ya bukaci ‘yan majalisar da su amince da karin Naira tiriliyan 3.557 baya ga Naira biliyan 442.72 da aka tanada a kasafin kudin 2022 na tallafin mai

Majalisun dokokin kasar nan sun amince da bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bijiro da ita na ware naira tiriliyan 4 na kudin tallafin man fetur, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Majalisar dattawa da ta 'yan majalisu sun amince da bukatar shugaban kasar ne bayan sun yi la’akari da rahotannin kwamitocinsu kan harkokin kudi.

Kara karanta wannan

Wata uku da shiga 2022, majalisa ta amince da kasafin kudin 2022, za a ci bashin N965.42bn

Majalisar dokokin kasar nan
Yanzu-Yanzu: Majalisa ta amince da bukatar Buhari ta kashe N4tr na tallafin mai | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Amincewar ta biyo bayan bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sake fasalin kasafin kudin shekarar 2021.

A yayin mika bukatar sake duba tsarin kashe kudaden, shugaban kasar ya bukaci ‘yan majalisar su amince da karin Naira tiriliyan 3.557 baya ga Naira biliyan 442.72 da aka tanadar a cikin kasafin kudin shekarar 2022 na tallafin, inji rahoton The Guardian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majalisar ta kuma amince da rage yawan danyen mai daga ganga miliyan 1.8 a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.6 a kowace rana da kuma tsara ma'auni na farashin mai na dala 73.

Mai neman Shugaban kasa ya ce Najeriya za tayi takara da Amurka idan ya samu mulki

A wani labarin na daban, Sanata Orji Uzor Kalu ya cika baki cewa karfin tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a cikin shekaru hudu muddin ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci

PM News ta rahoto shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan ya na wannan alkawari a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da shi a garin Abuja.

A cewar Orji Uzor Kalu, karfn GDP na Najeriya zai zama tamkar na Amurka, Jafan da sauran manyan kasashen Duniya, idan ya karbi shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.