Shugaba Buhari ya bada izinin fitar da kudi N1.4bn don inganta wutan lantarki
- Shugaban kasa ya amince da fitar da kudi kimanin bilyan daya da rabi don inganta wutan lantarki
- Za'a yi amfani da kudaden wajen gina gonar lantarki a Kaduna wanda zai kai jihar Filato, Jos
- Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki wanda ke muni idan wutar kasar ta lalace gaba daya
Abuja - Majalisar zartaswar tarayya ta amince da fitar da kudi N1.4bn don sayan kayayyaki ga kamfanin rarraba wutan lanarkin Najeriya, don inganta wutan lantarki a Najeriya.
Ministan Lantarki, Abubakar Aliyu, ya bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartaswar da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, rahoton Punch.
Yace:
"Na gabatar da wasu kudirorin ma'aikatar lantarki biyu na kamfanin raba wuta a Najeriya TCN."
"Na farko shine kwangilan 132/33 KV a Kafanchan, jihar Kaduna wanda zai kai Jos, jihar Flato na kudi N132,705, 861.42."
"Manyan kayayyakin aiki ne da TCN ke bukata don ayyukanta na gida da waje, hakazalika an amince da sayan Taransfoman tafi da gidanka."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa lalacewar wuta dake gudana kwanakin nan aikin yan zagon kasa ne marasa son cigaba ga Najeriya, riwayar TheCable.
Ministan yace sau tari an kai hari kan yan kasashen waje dake ayyuka kuma hakan na jinkirta kammaluwan ayyuka.
Barna a hasumiyar rarrabe wutar lantarki ce ta kai ga lalacewar wutar Ƙasa, FG
Ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a ranar Asabar ta ce lalacewar wutar lantarkin kasar nan ya biyo bayan barna da ake yi wa kasar a hasumiyar rarrabe wutar lantarkinta.
TheCable ta ruwaito cewa, wutar Najeriya ta lalace a ranar Juma'a, karo na uku a cikin makonni kadan, lamarin da ya jefa wasu jihohin kasar cikin matsalar wutar lantarki.
Da farko da, ma'aikatar wutar lantarkin ta ce tana bincikar dalilin lalacewar wutar kasar
Asali: Legit.ng