Kotu ta ce mai neman Gwamnan Kano a APC zai sake shari’a da EFCC kan zargin damfara

Kotu ta ce mai neman Gwamnan Kano a APC zai sake shari’a da EFCC kan zargin damfara

  • EFCC tayi nasara a karar da ta shigar a kan Abdulsalam Abdulkarim Zaura a kotun daukaka kara
  • Lauyan Hukumar ya yi dace Alkalai sun amince a sake sauraron shari’ar su da Abdulsalam A. Zaura
  • Abdullahi Bayero da sauran Alkalan da suka saurari karar sun yi fatali da hukuncin da Allagoa ya yi

Kano - A ranar Laraba kotun daukaka kara da ke zama a jihar Kano ta yanke hukunci a sake yin shari’a da Abdulsalam A. Zaura kan zargin da ake yi masa.

Jaridar The Cable ta ce ana zargin Abdulsalam A. Zaura da laifin satar fiye da $1,320,000. Zaura yana cikin masu neman kujerar gwamnan jihar Kano a APC.

Tun a 2018 aka ji hukumar EFCC ta gurfanar da A.A. Zaura a wani babban kotun tarayya da ke Kano bisa zargin ya damfari wani kamfani a kasar Kuwait.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Kamar yadda aka rahoto, ana zargin ‘dan siysar ya yiwa kamfanin karyar cewa ya na harkar gine-gine a Dubai, Kuwait da kuma wasu kasashen Larabawa.

Kotu ta wanke Zaura, amma bai fita ba

A shekarar 2020 ne Alkali Lewis Allagoa ya wanke Zaura, ya ce bai samu ‘dan siyasar da laifin da ake zarginsa ba. Hakan ta sa aka yi watsi da wannan kara.

Amma EFCC ba ta gamsu da hukuncin na Lewis Allagoa ba, wannan ya sa lauyan da ya tsayawa hukumar, Musa Isah ya daukaka kara zuwa kotu na gaba.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano tare da Abdulsalam A. Zaura Hoto: dimokuradiyya.com.ng
Asali: UGC

Lauyan ya fadawa kotu cewa A.A Zaura bai nan sa’ilin da Alkali ya wanke shi. Kotun koli kuma ta ce dole wanda ake zargi ya halarci shari’ar da ake yi da shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya maka Ministan shari’a gaban Alkali, ya na neman a biya shi N1.5bn

Jaridar ta ce kotun daukaka kara ta gamsu da hujjar da lauyan ya kawo, don haka ta karbi kararsa.

Alkalan kotun daukaka kara sun yi hukunci

A zaman da Alkalai uku na babban kotun suka yi a ranar Laraba, dukkansu sun yi fatali da hukuncin da Allagoa ya yi shekaru kusan biyu da suka wuce.

Abdullahi Bayero shi ne Alkalin da ya karanto hukunci a madadin sauran Alkalan, ya bada umarni a nemi wani sabon Alkali dabam da Allagoa ya saurari karan.

“Bayan an yi hukuncin da ya goyi bayan wanda ya kawo kara, za a daukaka shari’a. An yi watsi da hukuncin shari’a mai lamba FHCK/CR2018/FRN da aka yi da Abdulsalam Abdulkarim a ranar 9 ga watan Yuni, 2020.”

- Alkali Abdullahi Bayero

Alherin Abdulsalam Abdulkarim Zaura

Kwanaki aka samu labari Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya yi alkawarin zai kashe N200m a kan yaran Kano da suke karatu a manyan makarantun kasar nan.

Duk wani dalibi daga jihar Kano da yake karatun gaba da sakandare zai iya tashi da gudumuwar N20, 000 da gidauniyar AA Zaura za ta raba a shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng