Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Ba Amurke Da Bindigu a Filin Jiragen Sama Na Mohammed Murtala a Legas

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Ba Amurke Da Bindigu a Filin Jiragen Sama Na Mohammed Murtala a Legas

  • Jami'an tsaro a filin tashi da sauka jiragen sama na Mohammed Murtala, MMIA, a Legas sun kama wani Ba Amurke da bindigu
  • Rahotanni sun nuna cewa mutumin da ba a bayyana sunansa ba ya shigo Najeriya ne daga Amurka amma bai sanar da cewa yana dauke da bindigu ba bisa tsarin doka
  • Majiya daga filin tashin jiragen saman na Mohammed Murtala ta tabbatar da cewa mutumin yana can hannun Immigration yana amsa tambayoyi

Jihar Legas - An kama wani dan kasar Amurka dauke da bindigu a filin tashi da saukan jiragen sama na Mohammed Murtala (MMIA) a Legas.

Fasinjan, namiji, (da aka sakaya sunansa) ya iso Najeriya ne a cikin jirgin United Airlines daga Houston, Amurka misalin karfe 10.10 na safe, rahoton Daily Trust.

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Ba Amurke Da Bindigu Filin Jiragen Sama Na Mohammed Murtala a Legas
Jami'ai Sun Kama Wani Ba Amurke Da Bindigu Filin Jiragen Sama Na Mohammed Murtala a Legas. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

An rahoto cewa fasinjan ya sauka ne ba tare da ya sanar da cewa yana dauke da bindiga ba kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanada ga masu dauke da makamai.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace dalibai 5 na kwalejin lafiya da ke Tsafe

An gano bindigun da suka hada da Handgun, Barreta da harsashi guda 26 masu tsawon 9mm ne cikin kayansa inda aka boye su.

Fasinjan yana dauke da fasfo na kasashe biyu; Ta Najeriya da kuma Amurka.

Wata majiya daga filin jirgin saman ya shaida wa Daily Trust cewa mutumin bai sanar da cewa yana dauke da bindiga ba bayan saukarsa.

Shauntvng ta rahoto cewa wata majiya ta bayyana cewa fasinjan yana da takardun izinin mallakar bindiga daga Amurka, amma ba a riga an tabbatar da sahihancinsu ba.

Jami'an Immigration suna yi wa fasinjan tambayoyi, za su mika shi gaba idan sun gama

A lokacin hada wannan rahoton, ana can ana yi wa fasinjan tambayoyi a ofishin hukumar Immigration da ke filin jirgin saman.

Kara karanta wannan

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

Majiyar ta ce:

"Jami'an Immigration ne suka kama fasinjan da bindigu yayin tantance matafiya. Jami'an na masa tambayoyi kuma za su mika shi hannun hukumomin da suka dace idan an gama.
"Bayan haka, mun gano fasinjan na da izinin zama dan kasashe biyu kuma yana da takardar izinin mallakar bindiga a Amurka amma ya kamata ya sanar a lokacin da ya iso Najeriya sai dai bai yi hakan ba. Sai dai, ba mu tabbatar da sahihancin takardunsa ba."

Sanarwar daga hedkwatar hukumar ta ce kwantrola na Legas, CIS Kemi Nandap ta bayyana cewa sahihan bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa mutumin ya shiga jirgi ne daga Houston kuma ya boye bindigun a jakarsa.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel