Ramadaniyyat 1443: Ko da Mun Yi Saɓani, Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Ko da Mun Yi Saɓani, Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Ko da Mun Yi Saɓani......

1. "Lallai Allah (SWT) ya aiko Annabi Muhammadu SAW) da gaskiya, ya kuma saukar masa da littafi (Alƙur'ani). Ya aiko shi zuwa ga wasu mutane masu mabanbanta soye-soyen zukata, masu mabanbanta ra'ayi. Sai ya haɗa kawunansu da zukatansu, ya kuma ba su kariya daga Shaiɗan.

2. Allah (SWT) ya bayyana cewa, haɗin kan al'umma jigo ne da addininsa. Don haka, Annabi (SAW) ya kasance yana nuna wa sahabbansa rashin yardarsa da duk wata jayayya da za ta haifar da ɓaraka da sabani. Ya kuma sifanta kunƙigiya mai tsira da cewa, su ne jama'a, (watau wadanda suka haɗa kansu).

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

3. Malamai daga cikin sahabbai da tabi'ai da waɗanda suka zo bayansu, idan suna jayayya a kan wani al'amari sukan bi umarnin Allah inda yake cewa:

(Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar ƙarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyan makoma.).

Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Ramadaniyyat 1443: Ko da Mun Yi Saɓani, Daga Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Asali: Facebook

4. Sukan kasance sukan tattauna a kan wata masa'ala, tattaunawa ta neman shawara ko nasiha ga junansu.

5. Wani lokaci suka yi saɓani a kan wata mas'ala da ta danganci aƙida ko ibada, to amma suka wanzu da fahimtar juna da haɗin kai a tsakaninsu da 'yan'uwantakar addini.

6. Sabani a kan hukunce-hukuncen addini abu ne mai yawan gaske da ba zai lissafu ba. Idan ya zamanto duk sa'adda Musulmi biyu suka yi saɓani a kan wata mas'ala za su ƙaurace wa juna, to ba za a taɓa samun hadin kai ko 'yan'uwantaka a tsakanin Musulmi ba".

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

[Ibn Taimiyya, Majmu'ul Fatawa, juzu'i na 24, shafi na 170-175].

Asali: Legit.ng

Online view pixel