Yan bindiga sun harbe ɗan kasuwa har Lahira kwanaki kafin Ɗaura Aurensa

Yan bindiga sun harbe ɗan kasuwa har Lahira kwanaki kafin Ɗaura Aurensa

  • Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun harbe wani babban ɗan kasuwa a jihar Ebonyi mako ɗaya kafin ɗaura aurensa
  • Bayanai sun nuna cewa makasan sun halaka mutumin mai suna Chukwu a gaban matar da zai aura, suka kwace mata waya
  • Hotunan kafin aure da Mamacin da Budurwarsa da katin ɗaura auren su ya mamaye kafafen sada zumunta bayan mutuwarsa

Ebonyi - Yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa ɗan asalin jihar Ebonyi, Issac Nnaemeka Chukwu, mako ɗaya kafin ɗaura masa Aure, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Chukwu, mai sana'ar sayar da kayayyakin amfani, ya rasa rayuwarsa a hannun wasu da ake zargin masu kisan kai ne a Abakaliki, babban birnin Ebonyi, ranar Litinin da daddare.

Mamacin, wanda ya fi shahara da sunan Ochudo, ya fito ne daga yankin ƙaramar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba wasu kwamishinoni da hadimansa awanni 48 su yi murabus daga mukamansu

Issac Nnaemeka Chukwu.
Yan bindiga sun harbe ɗan kasuwa har Lahira kwanaki kafin Ɗaura Aurensa Hoto: @TheNation News
Asali: Twitter

Rahoto ya nuna cewa ya gama duk wasu shirye-shirye na Aurensa da budurwarsa, Favour Chioma, wacce take tare da shi lokacin da maharan suka kashe shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɗan uwa, wanda ya jiyo matar da Mamacin zai Aura na cewa an harbi Chukwu bayan ya rufe ɗaya daga cikin shagunan kasuwancinsa, ya nufi Mota zai shiga.

Punch ta rahoto ya ce:

"Yana da Shago a Kasuwar ƙasa da ƙasa inda yake kasuwancin kayayyaki. Ya mallaki wani wurin kuma a layin Chukwuma Ofeke, Ameke Aba."
"Lamarin a cewar matar da Marigayin zai aura ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na dare lokacin da suka kulle shago suka nufi Mota zasu shiga zuwa gida."
"Ba zato wasu mutane suka tare su, suka yi harbi a iska, suka umarci mutumin ya kwanta a ƙasa daga bisani suka harbe shi sau uku, suka kwace wayar matar suka yi gaba."

Kara karanta wannan

2023: Bayan samun ƙarin mutum biyu, yan takarar dake hangen kujerar Buhari a PDP sun kai 15

Yaushe ne ɗaura auren?

Hotunan Mamacin da matar da zai Aura na kafin aure ya watsu a kafafen sada zumunta biyo bayan mutuwar Angon.

Katin gayyatar daura Auren da ya bayyana ya nuna cewa an shirya ɗaura musu aure ranar 21 ga watan Afrilu, a gidan mahaifin matar dake Amaiyima Ekpelu, karamar hukumar Ikwo.

Kakakin hukumar yan sandan reshen jihar Ebonyi, Loveth Odah, ta ce hukumarsu ba ta da masaniyar abin da ya faru amma zata bincika sannan ta sanar a hukumance.

A wani labarin kuma Wasu muhimman Lokuta 5 masu Albarka da ya kamata Musulmi ya Amfana da su

Al'ummar Musulmai a faɗin Duniya sun kammala Goman farko ta Ramadana kuma tuni suka shiga Goma ta biyu.

Yayin da Musulmai suka jajirce wajen ayyukan Ibada da kai kukansu gaban Allah, mun tattaro muku wasu lokuta 5 masu muhimmanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262