ASUU ta zargi NITDA da Dr. Isa Pantami da kawo siyasa a yajin-aikin da ake yi a Jami'o'i

ASUU ta zargi NITDA da Dr. Isa Pantami da kawo siyasa a yajin-aikin da ake yi a Jami'o'i

  • Malaman jami’an Najeriya sun ce akwai yiwuwar yajin-aikin da su ke yi, ya kara daukar lokaci
  • Kungiyar ASUU ta bangaren Legas ta bayyana wannan a lokacin da ta zanta da manema labarai
  • Adelaja Odukoya ya na ganin Hukumar NITDA ta sa siyasa a game da gwajin da ake yi wa UTAS

Ogun - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta reshen jami’o’in yankin Legas ta yi magana a game da yajin-aikin da ya jawo aka rufe makarantun gwamnati.

Jaridar Punch ta ce shugabannin ASUU sun yi taro a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022 a jami’ar koyon aikin gona da ke garin Abeokuta, jihar Ogun.

Shugaban kungiyar ASUU na shiyyar, Adelaja Odukoya ya bayyana cewa ba za su janye yajin-aikinsu ba har sai gwamnati ta amince da manhajar UTAS.

Adelaja Odukoya ya ce dole sai gwamnatin tarayya ta cika duka alkawuran da ta yi wa malaman jami’a, kuma ta biya su bashin kudinsu kafin su koma aiki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan ɗalibai sun kwashe kwana 56 a gida, Gwamnatin Buhari ta shirya zama da ASUU

Da yake yi wa manema labarai jawabi a garin Abeokuta, Odukoya ya ce manhajar UTAS da suka kirkiro ta tsallake gwajin da aka yi, ta samu har maki 99.3%.

Akwai siyasa a batun - ASUU

An rahoto Odukoya ya na mai zargin gwamnatin tarayya da sa siyasa a lamarin jami’o’in kasar. Hakan ta sa ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su mara masu baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NITDA
Shugaban NITDA da wasu jami’an gwamnati Hoto: @NITDANigeria
Asali: Twitter
“Mu na so mu yi kira ga jama’a a game da murda labari da yada labaran karya da hukumar NITDA ta ke yi a kan gwaji da aiki da manhajar UTAS.”
“Kalaman kakakin NITDA za su iya jawo a cigaba da yajin-aiki, idan har gwamnati ta bari aka yaudare ta saboda rashin kwarewar jami’an NITDA.”
“Kungiyar mu ta na ganin cewa karshen rashin tausayi ne ga halin da jami’o’i, har da malaman jami’a da dalibai da daukacin kasar mu ta ke ciki.”

Kara karanta wannan

An soma bincike domin gano abin da ya jawo Goodluck Jonathan ya yi hadari a mota

- Adelaja Odukoya

Ministan sadarwa ya shiga zargi

Daily Trust ta rahoto shugaban kungiyar malaman jami’ar ya na cewa dole su fadawa mutanen Najeriya gaskiya a game da wannan manhaja da aka kawo.

Kungiyar ta na zargin cewa NITDA ta biyewa Ministan sadarwa, Dr. Ibrahim Isa Pantami wajen siyasantar da lamarin UTAS da ta tsallake duk wasu gwaji.

Zama Farfesan Pantami a FUTO

A 2021 ne Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya zama Farfesan tsaron kafofin yanar gizo a jami'ar tarayya da ke Owerri.

Kungiyar ASUU ta ce zaman Ministan Farfesa a lokacin da yake ofis ya saba ka'ida. ASUU ta ce a wajen ta Pantami ba Farfesa ba ne, domin bai cika sharudan ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng