An soma bincike domin gano abin da ya jawo Goodluck Jonathan ya yi hadari a mota

An soma bincike domin gano abin da ya jawo Goodluck Jonathan ya yi hadari a mota

  • FRSC za ta yi bincike da nufin gano abin da ya jawo tagawar Dr. Goodluck Jonathan ta yi hadari
  • Wani babban jami’in Hukumar a Abuja ya bayyana cewa an soma yin bincike a game da hadarin
  • Hukumar ta ce ana zargin direban motar shugaban kasar ya na zura gudu ne har mota ta kwace

Abuja - FRSC ta ma’aikatan hanya ta soma bincike domin gano abin da ya yi sanadiyyar da tawagar Goodluck Jonathan tayi hadari a kan titin Abuja.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Juma’a, 8 ga watan Afrilu 2022, da ya nuna cewa ana tunanin motocin tsohon shugaban kasar sun yi gudun ganganci ne.

Babban jami’in hukumar FRSC mai kula da shiryyar birnin tarayya Abuja, Samuel Ogar Ochi ya shaidawa Daily Trust wannan lokacin da aka yi hira da shi.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

Samuel Ogar Ochi ya tabbatarwa manema labarai cewa za a gudanar da cikakken bincike na musamman domin gano diddikin abin da ya kai ga hadarin.

Yadda abin ya auku - FRSC

Kamar yadda Ochi ya bayyana a madadin FRSC, wannan hadari ya auku da ayarin tsohon shugaban na Najeriya ne da kimanin karfe 2:45 na yamma.

Bugu da kari, Samuel Ochi ya ce an yi maza an dauke wadanda hadarin ya rutsa da su kafin jami’an hukumar FRSC su iya hallara inda tsautsayin ya auku.

Hanyar mota
Wani titi a Abuja Hoto: www.tori.ng
Asali: UGC

“A matsayina na babban jami’in hukumar FRSC na shiyyar birnin tarayya Abuja, na samu labari a game da hadari.”
“Sai na yi maza na wuce babban asibitin Abuja domin tabbatar da halin da wadanda hadarin ya rutsa da su, su ke ciki.”

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban EFCC Magu zai bar aiki, ya gagara samun karin matsayi zuwa AIG

“Daga abin da mu ka samu, akwai yiwuwar motocin su na gudu ne, ana gudun da ya jawo mota ta kubcewa direba.”

- Samuel Ogar Ochi

Har zuwa yanzu, an rahoto Ochi yana cewa wannan shi ne ra’ayinsu, amma daga baya komai zai fito fili idan har an kammala gudanar da binciken da ake yi.

A sanadiyyar hadarin, ‘yan sanda biyu sun mutu, yayin da wasu ‘yan sandan ke jinya a asibiti. Jaridar ta ce Ochi ya gana da jami’ai biyu da ke fama da rauni.

Sakon ta'aziyyar Jonathan

Ku na da labari cewa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya na hanyar komawa gidansa a Abuja daga filin jirgin saman Nnamdi Arzikwe na Abuja ne hadarin ya faru.

A jawabin da ya fitar, tsohon shugaban kasar ya ce hadarin ya yi sanadiyyar rasa wasu ‘yan sandan da ke gadinsa; Sufeta Ibrahim Abazi da kuma Yakubu Toma.

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng