Bidiyon dankareriyar budurwa tana watsi da abinci da zoben da saurayi ya bata na neman aurenta

Bidiyon dankareriyar budurwa tana watsi da abinci da zoben da saurayi ya bata na neman aurenta

  • Wani matashi 'dan Najeriya ya fuskanci tozarci yayin da yayi kokarin ba wa kuttubar budurwarsa mamaki ta hanya neman amincewa ta aureshi
  • Yayin da yasa guiwarsa daya a kasa yana mai mika ma ta zobe, matar harzuka yayi inda ta jefesa da zoben da abincin dake kan taburinsu a wani gidan cin abinci
  • Matar bata tsaya a nan ba, ta huce fushinta a kan wani mutumi da yayi kokarin shawo kan lamarin inda ta hargitsa wurin baki daya

Wani matashi 'dan Najeriya ya kwashi kashinsa a hannu yayin da yayi kokarin neman auren budurwarsa , inda ta ki yarda da bukartarsa ta hanyar cin zarafinsa.

@ourtalkroom ne suka wallafa yadda lamarin, ya auku a wani gidan saida abincin da ba a bayyana ba, wanda ya tada kura a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Kara karanta wannan

Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada

A bidiyon anga yadda mutumin ya sanya guiwarsa a kasa rike da zobe yayin da ya roki kuttubar budurwarsa ta amince ta aureshi.

Bidiyon dankareriyar budurwa tana watsi da abinci da zoben da saurayi ya bata na neman aurenta
Bidiyon dankareriyar budurwa tana watsi da abinci da zoben da saurayi ya bata na neman aurenta. Hoto daga @Ourtalkroom
Asali: Instagram

Matashin ya roki budurwar tasa a rashin sa a, bidiyon yadda lamarin ya auku ya matukar ba wa 'yan Najeriya mamaki, budurwar ta fusata dashi, tare da tuhumarsa a kan yadda ya kunyata ta da nuna bukatarsa na aurenta.

A lokacin da yake kan guiwarsa daya, ta kwace zoben auren gami da jifarsa da shi. Sannan ta cigaba da watsa masa abincin dake teburin gami da hargitsa wurin.

Wani mutum da yayi kokarin shawo kan lamarin ya samu nashi kason, yayin da kuttubar matar ta huce fushinta a kansa, sannan ta ki saurarar rokon da sauranyin ke ma ta.

Kara karanta wannan

Bayan kama matarsa da kwarto, dattijo ya tattara kayansa ya bar aurensu mai shekaru 30

Jama'a sun yi martani

Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a karkashin wallafar:

@femaleking_mel_288 ya ce: "A ina ka taba ganin an nemi auren irin wannan kuttubar ma?? Bama sa da hankali, ni abun ya bata min rai ma."
@veroomoagbedes31 ta ce: "Saboda kawai ita kuttubace yanzu sai ta auri wanda bai dace ba. Bafa ita ta halicci kanta ba. Duk da bai dace ba abunda tayi wa saurayin a bainar jama'a."
@ekpomasurprisehub ya ce: "Ba zan taba amincewa a antayamin ruwan lemo ba, abu mai sauki ne idan kin ce ba kya sona ki fadamin sannan ki tafi ba wai ki kwararamin wani abu ba, wannan alama ne na cin mutunci, ina shawartar saurayin da ya kyaleta sannan ya cigaba da rayuwarsa, sai ya hadu da wacce ta fita alkhairi."
@fadekeolude ya ce: "A yadda kike nan kamar biredin da ya fada ruwa, kin samu saurayin da ya shirya aurenki ya fito, ba kyason kama naki rabon."

Kara karanta wannan

Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin.

A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.

Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng