Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci, Sun bindige Sarkin Gargajiya har Lahira

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci, Sun bindige Sarkin Gargajiya har Lahira

  • Wasu tsagerun yan ta'adda sun halaka Basaraken Gargajiya a cikin Masallaci ranar Litinin da daddare a jihar Taraba
  • Lamarin wanda ya auku a garin Maisamari, mutanen yankin ne suka yi ta maza suka fatattaki yan bindigan
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai ba da bayani ba

Taraba - Yan bindiga sun farmaki Wani Masallaci a garin Maisamari dake ƙaramar hukumar Sardauna a jihar Taraba, suka kashe Hakimin yankin, Alhaji Abdulkadir Maisamari.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa Maisamari ya rasa rayuwarsa ne lokacin Sallan Isha'i ranar Litinin da daddare, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi nan take bayan sun kutsa cikin masallacin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Kaakin majalisar wakilai, dimbin yan majalisa sun dira birnin Madina aikin Umrah

Alhaji Abdulkadir Maisamari.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci, Sun bindige Sarkin Gargajiya har Lahira Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Haka nan, wasu bayanai sun nuna cewa mazauna garin ne suka yi kukan kura, suka afka wa maharan, hakan ya tilasta musu tsere wa zuwa cikin duwatsun dake kusa da garin.

Wani mazauni a yankin Musa Sale, ya faɗa wa jaridar cewa wasu mutane ne suka sadaukar da ran su, suka fuskanci yan bindiga kuma bisa tilas suka tsere kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa yan ta'addan ba su yi garkuwa da ko mutum ɗaya ba, kuma Hakimin da suka kashe an masa jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Wannan lamarin da ya auku a Maisamari ya zama na uku a jere da aka kai hari Masallaci a jihar Taraba a yan makonnin nan da suke shuɗe.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Kyari sun yi murabus daga majalisar dattawa

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai ba da cikakken bayani ba.

A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC da Sanata sun sanar da Buhari zasu shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Jiga-Jigan siyasa musamman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun shirya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanata Ibikunle Amosun na shirin sanar da shirinsu na neman kujera lamba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262