Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda

Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda

  • Rundunar yan sandan Najeriya a Abuja ta ce ta gano tushen harin da ya yi sanadin rasuwar shugaban Miyetti Allah
  • Kwamishinan Yan Sanda na Abuja, wadanda mambobin na MACBAN suka siyawar shanu ne suka bi sahunsu suka kai musu hari tare da kwace kudin
  • Rundunar yan sandan ta ce a halin yanzu ta yi nasarar gano tushen lamarin kuma bincike na tafiya amma ba za ta bayyana dukkan matakan da ta ke dauka ba

FCT, Abuja - Gwamnatin Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce ta yi bincike ta kuma gano wadanda suka kai wa mambobin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah hari a Gwagwalada, Abuja, rahoton The Punch.

A kalla mambobin kungiyar hudu ne ciki har da shugaban kungiyar aka kashe a makon da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

An rahoto cewa suna dawowa ne daga kasuwar Izom a Jihar Niger a lokacin da yan bindigan suka kai musu hari a kusa da kauyen Daku a Abuja.

Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda
Mun Tono Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

An kuma sace wasu mutane hudu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Sakatare Janar na MACBAN, Ngelzeerma Usman ya shaida wa wakilin The Punch cewa wadanda suka sace mutanen suna neman a biya fansar N100m.

Wadanda suka siya shanunsu ne suka bi sahunsu suka kai musu hari, Yan sanda

Da ya ke bada karin bayani kan lamarin, Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda bangaren ayyuka, Ben Igwe, ya ce maharan sun bi sahunsu ne suka kai musu harin, rahoton LIB.

Amma, ya ce yan sanda suna kan bincike.

Igwe ya ce:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Sha Kaye a Kotu, An Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamna Ayade Da Ya Koma Jam'iyyar APC

"Sun bi sahunsu ne suka kwace kudin da suka biya su bayan sun sayar musu da shanu. Muna aiki kan lamarin. Mun gano tushen abin kuma zamu tabbatar an kama su. Bana son bayyana abin da muke yi."

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164