Da Duminsa: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter Na 2022
- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin 15 da 18 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu don murnar bukukuwan Easter na bana
- Gwamnatin ta yi kira ga kiristoci su yi amfani da wannan damar domin yiwa kasa addu'a na samun zaman lafiya, tsaro da cigaba
- Sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya fitar ta kuma bukaci kiristoci su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Isah (AS)
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin hutu don murnar bukukuwan Easter a kasar, rahoton Daily Trust.
Easter biki ne da mabiya addinin Kirista ke yi domin murnar dawowar Annabi Isah (AS) bayan an giciye shi kuma ya mutu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya a ranar Talata kamar yadda ita ma The Guardian ta rahoto.
An bukaci kiristocin Najeriya su yi koyi da halayen Annabi Isah (AS).
A cikin sanarwar da Dr Shuaibu Belgore, Sakataren Dindindin na ma'aikatan ya fitar a madadinsa, Aregbesola ya bukaci kirista su yi koyi da halayen Annabi Isah (AS) da suka hada da sadaukarwa, yafiya, tausayi, kauna, hakuri, zaman lafiya.
Ministan ya bada tabbacin gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba sai ta kawo karshen yawaitan hare-hare da ake kai a a tituna, filin jirgin sama, jirgin kasa a kasar.
Ya ce:
"Tsaro hakki ne da ya rataya a kan kowa. Don haka ina kira ga yan Najeriya da yan kasar waje da ke zama a kasar su nuna kishin kasa a wannan lokaci mai muhimmanci ta hanyar goyon bayan jami'an tsaro a kokarinsu na kawo zaman lafiya da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al'umma."
Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.
Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.
Asali: Legit.ng