Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG

Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana kashe sama da bilyan goma a wata wajen ciyar da daliban makarantun firamare
  • Nan da yan makonni gwamnatin na sa ran daliban zasu karu kuma za'a koma kashe naira milyan 12
  • An fara shirin baiwa daliban makaranta abinci ne bayan hawar shugaba Buhari mulki a 2015

Abuja - Gwamnatin tarayya na kashe kimanin naira bilyan 10 a wata wajen shirin ciyar da daliban makarantun firamare a fadin tarayya.

Wannan aiki na gudana ne karkashin Ministar tallafi, jin kai, da jin dadin jama'a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Jagoran shirin, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan ranar Litinin, a taron warshan masu ruwa da tsaki na kwana biyu kan samar da takardar doka kan shirin, kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito.

Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG
Gwamnatin Buhari na kashe N10bn a wata wajen ciyar da dalibai, FG
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ramadana: Yadda kankara ta zama kamar nama a Kano saboda tsananin zafi

Dr Bindir ya bayyana cewa akwai muhimmancin a samar da takardar tsari kan shirin ciyar da dalibai don a samu cigaban shirin.

Yace ana ciyar da sama da dalibai milyan 10 a rana kuma N100 aka yi kiyasi kan kowani yaro a rana.

A cewarsa:

"Yau muna mayar da hankali ne kan shirin ciyar da daliban makarantun firamre tare hadin kan shirin abinci na majalisar dinkin duniya watau World Food Programme (WFP) don samar da takardar tsare-tsare."
"Wannan zai bada dama wajen samun cigaban shirin kamar da shugaban kasa yayi umurni."
"A yanzu haka muna ciyar da kimanin dalibai milyan 10 kuma nan da makonni da watanni zasu zama milyan 12."

Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya

Jagoran harkar tallafin majalisar dinkin duniya dake Najeriya, Matthias Schmale, ya bayyana cewa ana bukatar $351m don taimakawa al'ummar yankin Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Yadda cikin sati 2 Buhari ya magance matsalolin APC yayin da rashin tsaro ke cigaba

Matthias Schmale ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a taron janyo hankali kan abinci da kiwon lafiya a birnin tarayya Abuja.

Ya ce sama da yan Najeriya milyan 8.4 ke bukata tallafi a Najeriya, kuma babu kudi.

A jawabinsa yace a fadin Arewa maso gabashin Najeriya, mutum milyan 8.4 na bukatan tallafi. Abin takaici, rabin wannan mutane - 4.1m - zasu shiga halin bakin yunwa bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng