Kano: Rundunar 'yan sanda ta hana tashe a watan Ramadan ta bana a fadin jihar
- Rundunar 'yan sanda jihar Kano ta soke tashe a watan Ramadanan wannan shekarar saboda matsalar rashin tsaron da al'umma ke fuskanta
- Soke tashen ya zo ne bayan dubi da yadda hatsabibai ke amfani da damar wajen aiwatar da aikin ta'addanci a fadin jihar
- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi kira ga daukacin al'umma da su ja kunnen 'ya'yansu da kada su bari a kamasu da laifin karya doka don tabbatar da zaman lafiya
Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta haramta "Tashe", wani wasan barkwanci da ake yi duk shekara bayan kwanaki goma na farkon watan Ramadana.
Kakakin rundunar, SP Abdullaji Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a wata takarda da ta fita ranar Litinin, shafin LIB ya ruwaito.
Kamar yadda takardar ta bayyana, dalilin da yasa aka haramta al'adar mai cike da tarihi shine yadda hatsabibai ke amfani da damar wajen cutar da al'umma, Daily Trust ta ruwaito.
"Rundunar 'yan sandan jihar Kano na burin sanar wa da daukacin al'umma cewa ta dakatar da wasan barkwancin nan da aka dauki tsawon zamunna ana yi (Tashe), wanda ke zuwa duk bayan kwana goma na watan Ramadanan kowacce shekara.
"Dalilin hakan kuwa shine yadda hatsabibai ke badda kama da sunan "Tashe" don aikata munanan ayyuka irinsu sara-suka, kwacen waya, da ta'ammuli da miyagun kwayoyi."
Ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, ya yi kira ga mutanen kwarai na jihar Kano, musamman iyaye da marika da su jakunnen 'ya'yansu kada su yarda a kamasu da laifin karya kowacce irin doka da ka'ida.
"Duk wanda aka kama za'a yanke masa hukunci daidai da yadda shari'a ta tanada. Muna muku barka da fatan gama azumin watan Ramadana lafiya," ya kara da fadin haka.
Kano: Bene ya rushe, ya halaka rayuka 2, wasu 3 sun matukar jigata a Hotoro
A wani labari na daban, mutum biyu sun rasa rayukansu inda wasu ukun suka samu miyagun raunika masu barazana ga rayuwarsu bayan wani bene hawa daya da ake ginawa ya rushe a kwatas din Hotoro da ke Kano.
Mamatan biyu masu suna Aliyu Sulaiman mai shekaru 27 da Abdulganiyyu Sulaiman duk almajiran wata makaranta ne da ke kusa, Premium Times ta ruwaito.
Malaminsu ya sanar da Premium Times cewa, lamarin ya auku ne wurin karfe 3 na daren Asabar yayin da mamatan ke bacci a cikin kangon.
Asali: Legit.ng