Abuja ba ta zaman irinku bane: 'Yan sanda sun kama masu sana'ar 'Bola Jari'
- Rundunar 'yan sandan Abuja sun kama wasu mutane da ake zargi da sace kadarorin al'umma ba gaira ba dalili
- Rahoto ya bayyana cewa, mutane 98 ne aka kama suna kwasar kayayyakin jama'a da sunan sana'ar bola jari
- Rundunar 'yan sanda ta ce zata gufanar dasu a gaban kotu saboda zaman Abuja ba na irin nasu bane bata-gari
Jami’an ‘yan sandan Abuja sun kama wasu ‘yan bola jari 98 da aka fi sani da bisa laifin sata, tare da bayyana cewa Abuja ba ta zaman kowa ba ce, inji rahoton Vanguard.
Da yake jawabi yayin gabatar da wadanda ake zargin a ranar Litinin a hedikwatar rundunar, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Ben Igwe, ya bayyana cewa rundunar za ta tasa keyar wadanda ake zargin zuwa jihohinsu na asali.
DCP Igwe ya bayyana cewa wasu bakin mutane sun kutsa cikin babban birnin kasar, yana mai nuni da cewa rundunar tana ta kokarin gano irin wadannan mutane tare da korarsu daga Abuja.
Daily Post tattaro DCP na shaida manema labarai cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Abuja ba ta kowa ba ce. Mun umarce su da su je inda ya dace dasu.
“Muna kokarin ganin mun fatattake su daga FCT. Za mu ci gaba da yin haka kuma ba za mu ja da baya ba.
“Mun kwato wasu abubuwa da dama da bai kamata su samu ba. Suna satar kadarori yayin da suke ikirarin yin tattara bola.
“Mun nemi su bar garin. Jama’a da dama sun yi tururuwa zuwa FCT, wasu kuma suna zuwa ne da mugun nufi. Duk lokacin da kuka gansu, ku sanar da mu.
“Za mu kai su kotu domin tabbatar da an yi adalci. Muna da matsala mai tsanani a yanzu saboda barazana daga wurare da yawa."
Ku tuna cewa kimanin 50 daga cikin ‘yan bola jarin, da sanyin safiyar Litinin din nan, suka kai farmaki garin Kabusa, inda suka far wa mazauna garin tare da lalata kadarorinsu da gangan kafin ‘yan sanda su zo domin kwantar da lamarin.
Ni wai mai digiri: Na yi danasanin rashin iya sana'ar hannu, da yanzu na kudance a Kanada
A wani labarin, wani mutumin kasar Ghana mai suna Ben Sey ya magantu game da yadda rayuwarsa ta kasance bayan ya yi kaura daga Ghana inda ya ce ya yi danasanin rashin koyon sana’ar hannu kafin ya koma kasar waje da zama domin da shi ake kudancewa a kasar Kanada.
Da yake tuna halin da ya tsinci kansa, matashin ya kuma bayyana cewa ya yi karatu har zuwa matakin gaba da sakandare a Takoradi Polytechnic inda ya mallaki HND a bangaren zane-zane sannan ya samu damar tafiya waje bayan wasu shekaru.
Ya bayyana cewa yawancin mutanen da ake bibiya a aikin da yake yi a yanzu sune wadanda ke da gogewa a harkar sannan ya yi danasanin cewa bai taba koyon aikin hannu ba a Ghana.
Asali: Legit.ng