Karin bayani: Mummunar gobara ta ci mutane 5, ta kone jiragen ruwa 60 a jihar Ribas

Karin bayani: Mummunar gobara ta ci mutane 5, ta kone jiragen ruwa 60 a jihar Ribas

  • Yanzu muke samun labarin mummunar gobarar da ta auku a jihar Ribas, inda ta hallaka wasu mutane har biyar
  • Hakazalika, gobarar ta kone jiragen ruwa sama da 60, lamarin da har yanzu ba a san musabbabinsa ba
  • Sai dai, majiyoyi sun shaida cewa, watakila ajiye man fetur din da aka tace ba bisa ka'ida ba ne ya jawo gobarar

Jihar Ribas - Akalla mutane biyar ne da suka hada da mata biyu masu juna biyu da kuma jariri daya suka mutu a safiyar ranar yau Litinin bayan da wata gobara da ta tashi a wurin ajiye jiragen ruwa da ke Bonny/Nembe/Bille a Fatakwal ta jihar Ribas.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, haka kuma jiragen ruwa sama da 60 ne suka lalace a gobarar da aka ce ta fara a safiyar yau Litinin 11 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

Yadda gobara ta tashi ajihar Ribas
Da dumi-dumi: Mummunar gobara ta ci mutane 5, ta kone jiragen ruwa 60 a jihar Ribas | Hoto: channelstv.com
Asali: Depositphotos

Ko da yake ba a san musabbabin tashin gobarar, wanda shi ne na biyu cikin kasa da wata hudu, amma wasu mazauna yankin sun ce watakila ba za ta rasa nasaba da ajiyar man da aka tace ba bisa ka'ida ba a wurin ma'ajiyar jiragen.

Rahoton The Nation ya ce, wasu jiragen na fitar da man da aka tacen ne lokacin da gobarar ta tashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gobara ta tashi Babban Asibitin Asokoro da ke Abuja

A wani labarin na daban, wani sashi na babban asibitin yankin Asokoro da ke birnin tarayya Abuja ya kama da wuta, rahoton The Punch.

Ba bu tabbas ko an rasa rai sakamakon gobarar. Channels Television ta rahoto cewa daga bisani an yi nasarar kashe wutan.

Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, cikin wani sako da ta wallafa a Twitter ta ce: "Jami'an mu sun yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Babban Asibitin Asokoro a Abuja."

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun farmaki asibiti da kwalejin mata a jihar Borno

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.