Da Ɗuminsa: Allah Ya Yi Wa Ɗan Mai Cibiyar Markaz, Sheikh Adam Abdullahi Rasuwa

Da Ɗuminsa: Allah Ya Yi Wa Ɗan Mai Cibiyar Markaz, Sheikh Adam Abdullahi Rasuwa

  • Sheikh Ridwanullah, dan fari na Sheikh Adam Abdullahi Al Ilory mai Markaza ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayin ya rasu ne a safiyar raaar Asabar bayan sahur kamar yadda wata mjiya daga yanuwan suka sanar
  • Mutuwar Sheikh Ridwanullah na zuwa ne watanni biyu bayan Sheikh Sheikh Habeeb ya yanke jiki ya fari yayin wa'azi

Legas - Wanda ya kafa cibiyar koyar larabci da addinin musulunci ta Markaz, Agege, Jihar Legas, Sheikh Adam Abdullahi Al Ilory ya rasa ɗansa na farko, Ridwanullah.

Ya rasu ne a Legas a safiyar ranar Asabar kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa The Punch.

Da Ɗuminsa: Allah Ya Yi Wa Ɗan Mai Cibiyar Markaz, Sheikh Adam Abdullahi Rasuwa
Da Ɗuminsa: Allah ya yi wa ɗan Sheikh Adam Abdullahi na fari rasuwa. Hoto: The Punch/Sodiq Oyeleke.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shiekh Ridwanullah, wanda ya rasu bayan jinyar wata ciwo da ba a bayyana ba ya rasu ya bar ƴaƴa biyar.

Kara karanta wannan

Na shirya tsayawa gaban Allah ranar Lahira kan kalaman da na faɗa, Sheikh Khalid

"Eh, ya rasu. Ya rasu bayan Sahur. Mun masa sallah. Muna shirin zuwa birne shi," in ji ɗaya daga ƴan uwansa.

Sheikh Ridwanullah, wanda shine ɗan marigayi Adam Abdullahi Al Ilory, shima babban malamin addinin musulunci ne a kasar Yarbawa.

Ridwanullah ya rasu ne wata biyu bayan Sheikh Habeeb ya kamu da shanyewarsassan jikin

Within Nigeria ta rahoto mutuwar Ridwanullah na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan Mai Markaz, Sheikh Habeeb, ya kamu da ciwon shanyewar sassan jiki yayin wa'azi a Jihar Kwara.

Ciwon ya same shi ne a ranar 4 ga watan Fabrairun 2022 yayin daurin auren ƴar tsohon Alkalin Alƙalan Najeriya, Alfa Belgore.

An garzaya da malamin addinin zuwa asibitin koyarwa ta Jami'ar Ibadan don masa magani bayan ya yanke jiki ya faɗi.

Yayin da ya ke bayyana halin da ya shiga a ranar lakca na farko na watan Ramadan a ranar 2 ga watan Afrilun 2022, ya mika godiyarsa ga Allah.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

Habeeb ya yi bayanin cewa ya suma a lokacin da abin ya faru.

Kafin ya gama warware wa, ya ce wasu malaman za su cigaba da yin wa'azin.

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel