Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin gidan Kwmaishinan Filato, sun sace Iyalansa

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin gidan Kwmaishinan Filato, sun sace Iyalansa

  • Yan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan muhalli na jihar Filato a garin Gindiri, ƙaramar hukumar Mangu
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun sace mata da ɗiyar kwamishinan yayin harin wanda ya shafe kusan awa ɗaya
  • Wani shaida da abun ya faru a idonsa ya bayyana cewa maharan sun toshe hanyoyin garin yayin da ke aikata ɗanyen aikin

Plateau - Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da ɗiyar Kwamishinan muhalli na jihar Filato, Idi Bamayi.

Wata majiya daga iyalan kwamishinan ta shaida wa Channels tv cewa mutum biyun Mahaifiya da ɗiyarta sun shiga hannun yan ta'addan ne ranar Asabar da safe.

Majiyar ya ƙara da cewa yan bindigan sun kutsa har cikin gidan kwamishinan, daga bisa ni suka tasa Matarsa da ɗiyarsu zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Yan bindiga sun kai hari gidan Kwamishina a Filato.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin gidan Kwmaishinan Filato, sun sace Iyalansa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Iyalan sun tabbatar da cewa tuni suka kai rahoton abinda ya faru ga hukumomin tsaro a wani yunkuri na ganin waɗan da aka sace sun dawo gida lafiya.

Yadda lamarin ya faru

Wasu bayanai sun nuna cewa maharan sun kutsa da ƙarfin tsiya zuwa cikin gidan Kwamishinan, kafin daga baya sun sace mutum biyun a garin Gindiri, ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.

A cewar wani shaidan gani da ido, harin ya shafe kusan awa ɗaya yayin da yan bindigan suka toshe manyan hanyoyin garin, suka cigaba da aikata mummunan nufin su.

Ya ce:

"Harin ya ɗau dogon lokaci, kusan awa ɗaya, yan bindigan sun datse hanyoyin garin yayin da suke aikata nufin su."

Garin Gindiri da kewayenta sun jima suna fama da hare-haren yan bindiga a kai a kai a yan makonnin nan, inda aka yi garkuwa da mutane da dama.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, ASP Gabriel Ogaba, ya tabbatar da lamarin ga The Nation a Jos ya ce:

"Muna da masaniyar faruwar lamarin, tuni jami'an mu suka bazama farautar masu garkuwan, muna cigaba da kokarin ceto su."

A wani labarin kuma Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Delta, Ovie Agas, ya yi murabus daga kan kujerarsa kuma ba takara zai yi ba a 2023.

Kwamishinan yaɗa labarai, Mista Aniagwu, ya ce sauran kwamishinoni 9 da hadimai sun yi haka ne saboda shiga takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262