Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama

Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama

Wani rahoton da jaridar Punch ya fitar ya ce, wasu 'yan ta'adda sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a jihar Neja.

Rahoton ya tattaro cewa, an ce ‘yan ta’addan sun kai farmaki a unguwar Daza da ke karamar hukumar Munya ta jihar, inda suka yi ta harbe-harbe ba kakkautawa.

Yadda 'yan ta'adda suka farmaki jihar Neja
Da dumi-dumi: ‘Yan ta’adda sun kai farmaki a jihar Neja, sun sace mutane da dama | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mazauna garin da dama sun tsere daga yankin sakamakon harin da aka kai a daren jiya Alhamis.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.