Zambar Daukan Aikin Immigration: Kotu Ta wanke Abba Moro, ta kama Sakatariya da laifi

Zambar Daukan Aikin Immigration: Kotu Ta wanke Abba Moro, ta kama Sakatariya da laifi

  • Bayan shekaru takwas ana Shari'a, kotu ta wanke Sanata Abba Moro, amma ta kama Sakatariya da laifi
  • A 2014, ma'aikatar gwamnati ta karbi kudin fam daga hannun masu neman aikin Immigration amma akayi rub da ciki da kudaden
  • Gomman matasa masu neman aiki sun jikkata a filin jarabawar yayinda wasu suka rasa rayukansu

Abuja - Babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta wanke tsohon Ministan harkokin cikin gida, Abba Moro, bisa zambar daukan ma'aikata a hukumar shiga da fice watau Immigration.

Amma kotun ta kama sakatariyar din-din-din na ma;aikatar, Anastasia Daniel- Nwobia, da laifin zamba cikin aminci da yaudarar masu neman aiki.

Za ku tuna cewa a shekarar 2014, ma'aikatar harkokin cikin gida ta gudanar da jarabawa ga masu neman aikin Immigration inda cinkoso yayi sanadiyar mutuwar masu neman aiki akalla 14.

Kara karanta wannan

Ramadana: Yin azumi na karawa mutum karfi da lafiyar jiki – In ji kwararriyar likita

Cikin wadanda suka mutu akwai mace mai juna biyu.

Abba MorodaSakatariya da laifi
Zambar Daukan Aikin Immigration: Kotu Ta wanke Abba Moro, ta kama Sakatariya da laifi Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ma'aikatar ta karbi makudan kudi hannun masu neman aikin amma wasu yan tsiraru sukayi rub da ciki da kudin.

Bayan shekaru takwas ana Shari'a, kotu ta zabi ranar yanke mata hukunci.

Hukumar hana almundana da yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta bayyana hakan a jawabin da ta saki kuma Legit ta samu.

Jawabin yace:

"Mai shari’a Nnamdi Dimgba na kotun tarayya dake Abuja ranar Alhamis, 7 ga watan Afrilu, 2022, ya kama tsohuwa sakatariya ta dindindin ta hukumar cikin gida, Anastasia Daniel- Nwobia hukunci saboda laifin zamba a cikin neman aiki da hukumar shige da fice ta kasa ta nema a shekarar 2014.
Sai dai kuma mai shari’ar ya daga zuwa 17 ga watan Afrilu, 2022 a matsayin ranar da zai yanke mata hukunci.

Kara karanta wannan

Innalilahi: Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Gobara Da Ta Auku a Gidan Man Fetur a Jigawa

Tsohuwar sakatariyar na fuskantar tuhuma ne tare da tsohon ministan harkokin cikin gida Abba Morro, da Femi O alayebami, darakta a hukumar da wani Mahmood Ahmadu wanda ake nema ruwa a jallo da kamfanin Drexel Tech Nigeria Ltd.
Kotu ta kama Daniel-Nwobia da laifi a tuhuma ta hudu amma ta wanke Morro da Alayebami akan duk tuhumar."

Hukumar EFCC ta sha alwashin daukaka kara akan hukuncin da kotun ta yanke game da Abba Moro.

EFCC zata ladabtar da wasu matasa a Kano

EFCC ta damke wasu matasa shida da ake zargi da sace wa kakarsu miliyan N15.7 a jihar Kano.

Wadanda ake zargin Badaru Munir (23); Aliyu Falalu ( 23); AlMustapha Nasir( 22); Haruna Salisu Abatua( 23); Ismail Salisu Jibia (22), Ishaq Aminu (19), an damke su ne a wurare daban daban tsakanin 6 da 7 ga watan Maris, 2022.

An samu nasarar kama sune bayan wani Abdullahi Umar ya kai korafi cewa, wani lokaci a Satumba 2021, an cire kimanin N15, 708, 940 daga asusun bankin Union bank sannan aka tura shi izuwa wasu asusun banki daban daban.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel