Rudani da tashin hankali: An tsinci gawawwaki da harsasai jikinsu a wata gonar Abuja

Rudani da tashin hankali: An tsinci gawawwaki da harsasai jikinsu a wata gonar Abuja

  • Mazauna anguwar Kamadi cikin yankin Kwali dake birnin tarayya sun shiga firgici bayan an tsinci gawawwaki masu dauke da harsasai a wata gona
  • Mutanen anguwan sun zargi gawawwakin da zama na masu garkuwa da mutane ko kuma wadanda aka yi garkuwa dasu
  • Wani jami'in 'dan sandan yankin ya tabbatar wa manema labarai yadda aka kai daya daga cikin gawawwakin UATH na Gwagwalada, yayin da dayar gawar ta riga ta rube

Abuja - Mazauna anguwan Kamadi a yankin Kwali dake birnin tarayya (FCT) sun shiga rudani bayan an tsinci wasu gawawwaki guda biyu masu dauke da harsasai a wata gonar yankin.

Wani mazaunin yankin, Joshua Dogo, ya bayyana yadda a ranar Laraba wasu 'yan kauye, yayin dawowa daga gonarsu misalin karfe 5:00 na yamma suka ga gawawwakin guda biyu cikin wata gonar ayaba.

Kara karanta wannan

An Shawarci Al'umma Su Ƙauracewa Naman Shanu Na Sati Ɗaya Bayan Shanu 20 Sun Yi Mutuwar Ban Mamaki a Kogi

Rudani da tashin hankali: An tsinci gawawwaki da harsasai jikinsu a wata gonar Abuja
Rudani da tashin hankali: An tsinci gawawwaki da harsasai jikinsu a wata gonar Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya cigaba da bada labarin yadda suke zargin gawawwakin masu garkuwa da mutane ne ko kuma wadanda aka yi garkuwa dasu.

Wani jami'in 'dan sanda a marabar Kwali, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Daily Trust game da abunda aka gani, inda ya ce an aje daya daga cikin gawawwakin a asibitin koyarwa na Abuja (UATH) a gwagwalada.

Ya kara da cewa, "Dayar gawar ta riga ta rube. Muna jiran shugaban yankin ya amince wa sashin kula da muhalli damar birne gawar a wurin."

Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin martani, shugaban yankin, Danladi Chiya, ya ce za a amince da hakan kafin lokacin tashin aiki ya yi.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

A wani labari na daban, a kalla sojoji 11 ne aka kashe a mugun hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda majiya ta shaida wa TheCable.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

‘Yan bindigar da suka isa sansanin da yawansu sun kutsa cikin sansanin da ke kauyen Polwire a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi artabu da sojojin.

Majiyar soji ta shaida wa jaridar TheCable cewa, ‘yan bindigar sun bayyana a kan babura kuma suna dauke da manyan makamai da suka hada da gurneti (RPG).

Asali: Legit.ng

Online view pixel