Da Dumi-Dumi: Ban taɓa cewa ku zaɓi Buhari ba a 2015, Farfesa Soyinka

Da Dumi-Dumi: Ban taɓa cewa ku zaɓi Buhari ba a 2015, Farfesa Soyinka

  • Farfesa Wole Soyinka ya maida nartani ga masu sukarsa da cewa ya ba da gudummuwa wajen samun nasarar Buhari a 2015
  • Shahararren marubucin ya ce bai taɓa cewa ko ya ba da umarnin mutane su zabi wannan gwamnatin ba a wancan lokaci
  • A cewarsa, idan ya goyi bayan wani ai yana da damar hakan, kuma ya zama tilas ya yi magana idan ɗan takarar ya gaza

Lagos - Shahararren marubucin nan, Wole Soyinka, ya bayyana cewa ko sau ɗaya bai taɓa nuna goyon bayansa ga takarar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ba a zaɓen 2015.

Mista Soyinka a wurin wani taron manema labarai ranar Alhamis a Legas, ya ce bai samu damar kaɗa kuri'a ba a zaɓen 2015, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Farfesa Wole Soyinka.
Da Dumi-Dumi: Ban taɓa cewa ku zaɓi Buhari ba a 2015, Farfesa Soyinka Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Ba gaskiya bane ku ce na goyi bayan a zaɓi shugaba Buhari," Inji shi, inda ya ƙara da cewa abinda ya san harshensa ya faɗa shi ne, "Kada a zaɓi Goodluck Jonathan."

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

Farfesan ya ƙara da cewa yana da damar ya zaɓi ɗan takarar da zuciyarsa ta amince da shi, idan wannan mutumi ya gaza abin da ya kamata, ya na da damar magana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me ya jawo Soyinka ya yi wannan magana?

Yayin da ake fama da matsanancin tattalin arziƙi da rashin tsaro da ya mamaye sassan ƙasar nan, yan Najeriya da dama sun soki Soyinka bisa ba da gudummuwa wajen nasarar shugaba Buhari.

Farfesan ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, kamar yadda Punch ta rahoto.

Lokacin da siyasar 2015 ta ɗau zafi, Soyinka ya nesanta kansa daga rahoton kafafen watsa labarai waɗan da ke nuna yana goyon bayan wani ɗan takara.

A wata sanarwa da ya fitar a cikin watan Janairu, 2015, Soyinka ya ce:

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga

"Duk waɗan nan labaran da ake jingina mun ba gaskiya bane kuma wasu ne suka ɗauki nauyi domin su yaudari mutane."
"Duk lokacin da na zabi na goyi bayan wani ɗan takara, ina da cikakkiyar dama, amma zan tabbatar da na yi amfani da kafafen da zasu tabbatar da saƙon daga wurina ya fito.

A wani labarin kuma Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

Wata mata saboda tsabar kishi ta ɗaɓa wa Maigidanta wuƙa har lahira saboda ya shaida mata zai ƙara Aure daga kauyen su.

Lamarin ya auku a jihar Oyo, kuma rahoto ya nuna cewa Matar yar shekara 43 ta halaka Mijin ne yana tsaka da bacci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel