An damke dan sandan da ya kwace N50,000 hannun dan bautan kasa

An damke dan sandan da ya kwace N50,000 hannun dan bautan kasa

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta kama daya daga cikn jami'anta masu bata mata suna cikin al'umma
  • ASP Eyitere Joseph ya kwace kudi naira dubu hamsin hannun wani yaro mai bautan kasa a jihar Legas
  • Kakakin hukumar yan sandan Najeriya ya yi Alla-wadai da dabi'ar wannan jami'in dan sanda

Legas - Wani mataimakin sufritandan yan sanda, Eyitere Joseph, ya shiga hannun hukuma kan laifin kwace N50,000 hannun wani matashi dan bautan kasa a Legas.

Kwanakin baya aka daura bidiyon dan sandan da kudi a hannu a shafin Tuwita da ikirarin cewa ya karbi kudin hannun wani matashi a Ile Iwe, Ejigbo, jihar Legas.

An damke dan sandan da ya kwace N50,000 hannun dan bautan kasa
An damke dan sandan da ya kwace N50,000 hannun dan bautan kasa Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

Martani da bidiyon, Kakakin hukumar yan sanda, CSP Muyiwa Adejobi, @Princemoye1, ranar Laraba yace an damke dan sandan.

Kaakakin wanda yayi Alla-wadai da abinda dan sandan yayi ya ce an gudanar da bincike kan lamarin kuma za'a hukunta shi.

Yace:

"ASP Eyitere Joseph, da aka haska ya shiga hannu a Legas. Ana bincikensa kuma ana shirin hukuntashi."
"Yana aiki ne da yankin Meiran kuma an gargadi DPOn Meiran idan irin wannan abu ya sake faruwa sai an hukuntata bisa doka."
"Ku yarda da mu, zamu cika alkawuranmu a koda yaushe."
"Ta wani dalili magidanci zai cuci mai bautar kasa."

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

A wani labarin kuwa, tsohon shugaban rundunar binciken sirri, DCP Abba Kyari ya ki amsar abincin da aka ba shi a gidan gyaran halin da aka sakaya shi a ranar Litinin, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala: Martanin 'yan Najeriya kan hukuncin shekaru 24 da kotu ta yanke wa mulhidi

Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci abincin da matarsa ta kai masa ko kuma wanda wani cikin ‘yan uwansa ya kai masa.

Dama Kyari ya gurfana gaban kotu ne bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, kuma babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta ki bayar da belinsa.

Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA ta zargi Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda 4 da rufa-rufa da kuma harkar hodar ibilis mai nauyin 17.55kg.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng