Ba zamu buɗe jami'o'in Najeriya ba har sai an yi abun da ya kamata, inji ASUU
- Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya ta ce ba zata janye yajin aikin da take ba har sai gwamanati ta cika mata bukatunta
- Shugaban ASUU na shiyyar Kalaba da ya ƙunshi wasu jihohi, Aniekan Brown, ya ce ASUU ba ta damu jami'o'i su cigaba da zama a kulle ba
- Yace daman sun yi hasashen sakamakon gwajin UTAS duba da barazanar da kungiyar ta yi na fara yajin aiki
Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta ce ko kaɗan ba ta damu ba dan jami'o'in Najeriya sun cigaba da zama a kulle har sai gwamnati ta yi abinda ya dace domin gyara harkar ilimi da walwalar ma'aikata da ɗalibai.
The Nation ta rahoto cewa ASUU reshen shiyyar Kalaba wanda ya haɗa jihohin Akwa ibom, Cross Riba, Abia da Ebonyi, ita ce ta bayyana matasayarta a wata sanarwa.
Shugaban ƙungiyar ASUU na shiyyar, Aniekan Brown, yayin zantawa da manema labarai, ya ce:
"Ya zama wajibi mu jawo manema labarai domin bayyana matsayar ASUU kan batutuwan da ake kai ruwa rana da suka haɗa da yarjejeniyar FGN/ASUU 2009 da kuma rikicin IPPIS da UTAS."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kuma gwamnatin tarayya ba ta damu ba da yunkurin raunata abun da muka ƙirƙira a gida. Domin share tantama tsarin IPPIS da gwamnati ta kawo bai dace da tsarin jami'a ba."
"Bisa jajircewar ASUU kan ƙin yarda da IPPIS, gwamnati ta ƙalubalanci mu zo da wata hanyar da ta fi. ASUU ba ta yi ƙasa a guiwa ba duk da ƙuncin da aka shiga na Korona da sauransu, muka samar da UTAS."
Ya ƙara da cewa amma abin takaicin sai gwamnati ta sake ɓullo da wani abu na daban ta hanyar kawo wasu matsaloli na daban.
Ya sakamakon gwajin UTAS ya kasance?
A cewarsa dama sun yi hasashen amincewa ko akasin haka tun da gwamnati ta ce zata aiwatar da gwajin sahihanci a kan UTAS.
"Dama mun yi hasashen haka sakamakon zai kasance, duba da barazaanr tsunduma yajin aiki da ƙungiya ta yi a lokacin."
"Duk da samun kaso mafi tsoka da UTAS ya yi, amma sun yanke hukunci cewa ya faɗi a gwajin da suka ce sun gudanar."
A wani labarin na daban kuma Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Delta, Ovie Agas, ya yi murabus daga kan kujerarsa kuma ba takara zai yi ba a 2023.
Kwamishinan yaɗa labarai, Mista Aniagwu, ya ce sauran kwamishinoni 9 da hadimai sun yi haka ne saboda shiga takara.
Asali: Legit.ng