Dole malamai su dunga fadar gaskiya kan halin da Najeriya ke ciki – Sheikh Khalid
- Babban limamin masallacin Juma'a ta Apo da ke Abuja da aka sallama, Sheikh Nuru Khalid ya kalubalanci malamai da su kasance masu fadar gaskiya
- Shehin Malamin ya ce ya zama dole a samu karin malamai da za su dunga fitowa su yi magana a kan mummunan halin da kasar Najeriya ke ciki a yanzu
- Sheikh Khalid ya kuma zargi Sanata Dansadau da amfani da mumbarin masallaci wajen bayar da kariya ga gwamnatin APC mai ci a yanzu
Shugaban gidauniyar bincike da Da’awar Musulunci, Sheikh Nuru Khalid, ya ce limamai kadan ne ke da kwarin guiwar yin magana a kan mawuyacin halin da kasar ke ciki a yanzu.
Daily Trust ta rahoto cewa Shehin malamin ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a wani shirin Trust TV na ‘Daily Politics’a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu.
An dakatar da Sheikh Khalid, wanda ya kasance babban limamin masallacin Apo da ke Abuja, sannan daga baya kwamitin masallacin ya sallame shi gaba daya saboda ya soki gwamnatin Buhari a hudubarwa.
Sheikh Khalid ya hori malamai da su zama masu fadar gaskiya
Babban limamin ya bukaci malamai da su dunga fadar gaskiya koda kuwa a kan kowanene.
“Limamai yan kadan ne ke magana kan mummunan halin da ake ciki a kasar nan. Kuma yanzu ne lokacin da ya kamata a magantu. Idan kai limami ne, kada ka ji tsoro. Ka fadi gaskiyar zance sannan ka bari su kwace masallacinsu.”
Sheikh Nuru Khalid ya ce a kafofin watsa labarai ya fara samun labarin dakatar da shi da aka yi.
Ya ce:
“Aikin mutum daya ne, domin babu kwamitin da ya zauna kafin dakatarwar da ake magana a kai. Idan da suna so na tafi, da sai su tunkare ni gemu da gemu kuma da zan yi haka cikin mutunci. Babu abun da zan rasa.”
Daily Trust ta kuma rahoto cewa malamin ya ce ba gwamnati bace ke da masallacin kamar yadda kwamitin Musulmai a kwatas din yan majalisa suka bayyana.
A halin da ake ciki, limamin ya zargi Sanata Dansadau da amfani da mimbarin masallacin wajen kare gwamnati mai ci.
Ya kara da cewar:
“Ina a Jos lokacin da taron jama’a suka yiwa Dansadau ihu saboda dabi’arsa ta kare gwamnati. Wannan shine mutumin da ya soki sauran gwamnatoci a kan mumbarin.”
Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid
A baya mun ji cewa Sheikh Nuru Khalid, ya ce sukar da yake yiwa gwamnati kan gazawarta ba sabon abu ba ne.
Malamin wanda kwamitin masallacin ya sauke bayan ya soki gwamnatin Buhari, ya ce sama bai rikito ba a lokacin da ya yi Allah-wadai da rashin tsaro a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Legit Hausa ta rahoto cewa an dakatar da malamin ne saboda hudubar da ya yi kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashe a kasar.
Asali: Legit.ng