'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

  • Gwamnatin Tarayya ta ce yan ta'adda da suka kai hari sansanin sojojin Najeriya da ke Kaduna ba su ji da dadi ba
  • Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu ya ce sojoji sun kashe da dama cikin yan bindigan yayin dakile harin
  • Mohammed ya zargi kafafen watsa labarai da karfafa wa yan bindiga gwiwa ta hanyar wallafa labaransu a shafukansu na farko

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Zargin hari a Abuja: An baza sojoji a ko'ina saboda su dakile harin 'yan bindiga

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
Lai Mohammed: 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Mohammed, wanda ya ce batun tsaro a sassan kasar bai fi karfin gwamnati ba akasin abin da mafi yawancin mutane ke zato, ya ce ba dukkan nasarorin sojoji kan yan ta'adda ake wallafawa a kafafen watsa labarai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lai Mohammed ya zargi kafafen watsa labarai da haskaka labaran yan ta'adda

Daily Trust ta rahoto cewa ya zargi kafafen watsa labarai da karfafa wa yan ta'adda gwiwa ta hanyar wallafa labaransu a shafukan farko na jaridu.

Ministan ya kuma zargi jam'iyyar PDP da laifin shuka yunwar da a yanzu yan Najeriya suke fama da ita yayin da ya ke amsa wata tambayar kan tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari

Ya ce duk da kallubale daban-daban da ake fuskanta, gwamnati mai ci yanzu tana yin duk mai yiwuwa don magance matsalar.

Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus

A bangare guda, tsohon shugaban sojin Najeriya na daya daga cikin jihohin arewa ya ce babban abinda ya ke janyo hauhawar rashin tsaro musamman a yankin arewa shi ne rashin jagorori na kwarai, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda ya shaida, idan aka samar da makamai masu kyau ga sojojin Najeriya, cikin watanni 6 za a gama da ‘yan ta’adda.

A cewarsa:

“Zuwa yanzu, na yarda da cewa ‘yan Najeriya sun fahimci cewa sun yi babban kuskure na zaben Buhari kuma sun gane cewa ba zai iya wani shugabancin a zo a gani ba a kasar nan.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164