Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin bude baki, sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da wasu
- Wasu tsagerun yan bindiga sun kai mumunan hari Masallacin lokacin Sallar Magariba a jihar Taraba
- Akalla mutum uku suka rasa rayukansu a harin yayinda aka sace wasu
- Jihar Taraba dake Arewa maso gabas kwanakin nan na fuskantar barazanar yan bindiga masu garkuwa da mutane
Bali, Taraba - Yan ta'adda masu garkuwa da mutane sun kai hari Masallaci ranar Talata yayinda Musulmai ke bude baki inda suka hallaka akalla mutum uku kai tsaye.
Rahoton Daily Trust ta nuna cewa yan bindigan kimanin su guda hamsin sun dira Masallacin ne da Magariba kuma suka yi awon gaba da dimbin mutane.
An tattaro cewa wannan abu ya faru ne a garin Baba Juli, karamar hukumar Bali ta jihar Taraba.
Wani mazaunin garin wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa:
" Harin jiya ya bamu mamaki. Muna shan ruwa cikin Masallaci yayinda muka fara jin harbin bindiga kuma babu abin da muka iya."
Ya ce akalla mutum uku suka rasa rayukansu cikin Masallacin kai tsaye kuma an yi awon gaba da wasu.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da labarin amma bai bada bayani ba.
Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus
Tsohon shugaban sojin Najeriya na daya daga cikin jihohin arewa ya ce babban abinda ya ke janyo hauhawar rashin tsaro musamman a yankin arewa shi ne rashin jagorori na kwarai, Daily Trust ta ruwaito.
Kamar yadda ya shaida, idan aka samar da makamai masu kyau ga sojojin Najeriya, cikin watanni 6 za a gama da ‘yan ta’adda.
A cewarsa:
“Zuwa yanzu, na yarda da cewa ‘yan Najeriya sun fahimci cewa sun yi babban kuskure na zaben Buhari kuma sun gane cewa ba zai iya wani shugabancin a zo a gani ba a kasar nan.”
Asali: Legit.ng