Gwamnati za ta baiwa matasa guda 98,000 bashin kudin N50,000 zuwa N300,000: Sadiya
- Gwamnatin Buhari za ta rabawa yan Najeriya kusan dubu dari kudin bashi don taimakawa kasuwancinsu
- Duk wanda aka baiwa kudin ya sani ba kyauta aka bashi ba, bashi ne kuma zai biya nan da watanni tara, Sadiya tace
- Wadanda za'a baiwa bashin sun hada da manoma da yan kasuwa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirin baiwa yan Najeriya mutum 98,000 bashi maras kudin ruwa cikin tsarin Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP) 2.0.
Ministar walwala, tallafi da jin dadin mutane, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Anibeze, ta fitar ranar Laraba, rahoton NAN.
Hajiya Sadiya ta ce wadanda aka zaba zasu samu bashin kudi N50,000 zuwa N300,000.
Tace wadanda aka zaba zasu samu sakon taya murna nan ba da dadewa ba.
Ta kara da cewa duk wanda aka baiwa kudin ya san ba kyauta aka bashi ba, bashi ne kuma zai biya nan da watanni tara.
Tace:
"GEEP 2.0 wani tsarin bashi ne da gwamnatin tarayya ke badawa ga talakawa da masu nakasa."
"Bashin ya hada da kananan yan kasuwa karkashin shirye-shiryenta guda uku."
“shirye-shiryen sune MarketMoni, TraderMoni da FarmerMoni.
"Wannan ba kyauta bane. Bashi ne mara ruwa da ya zama wajibi a biya cikin wata tara.
Hajiya Sadiya ta ce ma'aikatar na shirin fara raba kudin kuma daga baya a dauki bayanansu.
Yan Najeriya miliyan biyu zasu fara karɓan Biliyan N20bn wata-wata daga Yuni, FG
A wani labarin kuwa, Gwamnatin tarayya tace zata fara raba wa yan Najeriya Naira Biliyan N20bn daga watan Yuni a tsarin tallafi karkashin shirin National Cash Transfer, kamar yadda Punch ta rahoto.
Bayanai sun nuna cewa FG zata biya yan Najeriya miliyan biyu N5,000 a shirin 'Basic Cash Transfer' da kuma ƙarin N5,000 a tsarin tallafawa talakawa. Jimulla FG zata kashe biliyan N20bn kan mutanen da zasu amfana.
Wani bayani da ya fita a watan Maris, 2022 kan dabaru da kuma tsarin harkokin ma'aikatar jin ƙai da walwalar al'umma ya nuna cewa yan Najeriya dake amfana da shirin ƙara ƙaruwa suke.
Asali: Legit.ng