Tashin hankali: An watse a coci yayin da fasto ya mutu yana tsaka da caccakar matsafa
- Rahoto ya bayyana yadda wani Limamin coci ya mutu yayin da yake wa'azi kan masu neman kudin wuri
- An tattaro cewa, limamin ya caccaki mutanen da ke tsafi domin samun kudi, inda ya yi tsokaci game da mutuwa
- Lamarin ya tada hankalin jama'a, inda aka zarce dashi asibiti kai tsaye, amma rai ya yi halinsa nan take
Abeokuta, Ogun - Wani Limamin cocin Evangelical Winning All da ke Onikoko ta Abeokuta a jihar Ogun, Francis Ogunnusi, ya mutu yayin da yake wa’azi a coci ranar Lahadi.
Marigayin ya kasance Baale na unguwar Onikoko, kusa da yankin Panseke a Abeokuta, inji rahoton jaridar Punch.
An tattaro cewa Ogunnusi yana kan mimbari ne a ranar Lahadi yana caccaka wa’azin yaki da cutar nan ta 'kudin wuri' da ya zama ruwan dare a sassan kasar nan.
An ga wani faifan bidiyon da Daily Post ya yada, inda aka ji mamacin yana gargadin masu kashe mutane domin su yi arziki, inda ya ce idan sun mutu wasu ne za su cinye kudin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ogunnusi, a lokacin da yake wa’azi da harshen Yarbanci, ya ce:
“Kudin da kuke samu ta haramtacciyar hanya, kuna kashe mutane, kuna shan jinin mutum, idan mutuwa ta zo, na wani ne.”
Sai kwatsam, yayin da mai fassarar kalamansa a cocin zuwa harshen Ingilishi ke aikinsa, Ogunnusi ya fadi da makirufo a hannunsa.
Hakan ya haifar da hayaniya a zauren cocin, yayin da mutane suka garzaya da shi asibiti.
Wani dan cocin da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce an garzaya da mamacin zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Idi Aba a Abeokuta, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Wanene mamacin?
Majiyar ta ce:
“Mutumin ba limamin cocin ba ne; dattijo ne kawai. Shi ne Baale na Onikoko. Shi ne ya yi wa'azi a ranar Lahadi.
“Yana magana ne game da mutuwa da kuma mutanen da suka samu kudi ta hanyar kashe wasu mutane. Kwatsam sai ya fadi. An garzaya da shi asibitin FMC, inda ya rasu. Ba mu san abin da ya faru ba. Na ji tsoro sosai. Komai ya lalace. Muka yi addu'ar alheri muka tafi gida."
Majiyar ta kasa tantance ko Ogunnusi na da wani rashin lafiya kafin faruwar lamarin, inda ta kara da cewa marigayin ya kai shekaru 60 zuwa 70 a duniya.
An tattaro cewa cocin da ke Onikoko hedikwatar ECWA ce a jihar Ogun.
An ce an ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa ta asibiti.
Damfara: An kama 'yar shekara 24 da ta addabi Kanawa da sata da katunan ATM
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa ‘yar shekara 24 mai suna Osasi Chinozom Juliet bisa laifin damfarar mutane ta katunan ATM din su, inji rahoton DailyTrust.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an kwato fiye da katunan ATM guda 15 daga hannun Juliet da ake zargi.
Legit.ng ta kuma tattaro cewa Juliet ta kasance cikin jerin sunayen wadanda hukumar 'yan sandan jihar Kano ke nema kafin a kama ta.
Asali: Legit.ng