Sunaye: Jerin kasashen duniya 5 masu tarin biloniyoyin duniya
- A shekarar 2022, mujallar Forbes ta gano jerin biloniyoyi 2,668 a duniya wadanda arzikinsu ya kai $12.7 biliyan zuwa sama
- Sai dai, akwai kasashen duniya biyar da suka hada da Amurka, China, India, Rasha da Jamus inda biloniyoyin suka fi yawa
- Daga cikin biloniyoyin duniya, Elon Musk ne ke kan gaba inda ya fi kowa arziki a fadin duniya baki daya
Kamar yadda jerin biloniyoyi na duniya da Forbes ta fitar karo na 36 ya nuna, akwai biloniyoyi 2,668 masu arzikin $12.7 tiriliyan a duniya. Duk da yaki, annoba da kuma tashin kadarori a kasuwanni, hakan bai girgiza wadannan mashahuran masu arzikin na duniya ba.
An gano biloniyoyi 2,668 a fadin duniya a 2022 kasa da 2,755 da aka samu a 2021 masu dukiya wacce ta kai darajar $12.7tirliyan kasa da $13.1 tiriliyan.
Kasashen duniya biyar ne suka samar da yawancin biloniyoyin duniya. Babu wanda ya wuce Elon Musk a arziki, wanda shi ne yanzu ya fi kowa kudi a duniya kuma wannan ne karon farko da ya fara kaiwa wannan matsayin.
Ga wasu daga cikin kasashen duniya da ke da tarin biloniyoyi:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Amurka
Har a halin yanzu Amurka na cigaba da tunkaho da biloniyoyi 735 a duniya, sun samu karin 11 fiye da shekarar 2021.
2. China
China ce kasa ta biyu da ke da tarin biloniyoyi inda suka kai 607 a biranen Hong Kong da Macau.
3. India
Kasar Indiya ce ke biye da China inda ta mallaki biloniyoyi 166 na duniya. Mukesh Ambani na kasar India har yanzu shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Asia.
A kiyasi dukiyarsa ta kai $90.7 biliyan. Ambani ne ya ke a matsayin mutum na 10 da ya fi kudi a duniya inda da kadan ya wuce Gautam Adani na kasar India wanda arzikinsa ya karu da $40 biliyan wanda jimillar ya kai $90 biliyan bayan hannayen jarin kamfanoninsa sun yi tashin gwauron zabi.
4. Jamus
Kasar Jamus ta zo a kasa ta hudu a duniya da ta fi yawan biloniyoyin duniya inda ta ke da mutum 134.
5. Rasha
Rasha ta bayar da gudumawa ga jerin biloniyoyin duniya inda 'yan kasar ta 83 suka hau wannan matakin.
TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido
A wani labari na daban, kusan watanni biyu da suka gabata, fitaccen hazikin mawakin Najeriya, Davido, ya siya wa kansa sabon gida a Banana Island da ke Legas kuma yayi liyafa saboda hakan.
A wallafar kwanan nan, mawakin ya bayyana wasu sassan ciki da wajen katafaren gidan nashi.
Daga cikin katafaren gidan mawaki Davido, an kawatar da shi da haske masu kyau, kujeru, zane, kayan kawa da kuma wasu daga cikin lambobin yabon da ya taba karba.
Asali: Legit.ng