Innalilahi: Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Gobara Da Ta Auku a Gidan Man Fetur a Jigawa
- Mutanen karamar hukumar Kaugama a Jihar Jigawa sun shiga zaman makoki sakamakon mutuwar wasu mutane bakwai
- Mutanen bakwai sun riga mu gidan gaskiya ne sakamakon mummunan gobarar da ta tashi a gida man fetur na Al-Masfa
- Mr Adamu Shehu, mai magana da yawun hukumar NSCDC ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce kawo yanzu ba a san musababin gobarar ba
Jigawa - Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Jigawa ta tabbatar cewa mutane bakwai sun mutu sakamakon gobara da ta barke a gidan mai na Al-Masfa da ke karamar hukumar Kaugama a Jihar Jigawa, rahoton The Punch.
Kakakin rundunar, Mr Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata a Dutse, ya shaida wa manema labarai cewa ba a tabbatar da sanadin gobarar ba a lokacin hada wannan rahoton.
Shehu ya yi bayanin cewa jami'an hukumar ta NSCDC da wasu hukumomin tsaron ne suka hada kai wurin kashe gobarar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Gobarar ta lashe wani gini da ke dauke da ofisoshi da gidajen wasu daga cikin masu aiki a gidan man fetur din.
"Abin bakin ciki, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa suna barci yayin da wasu suna hutawa bayan kammala aikinsu na ranar.
"Sakamakon hakan, mutum shida cikin wadanda abin ya shafa sun mutu nan take yayin da dayan kuma ya rasu bayan an garzaya da shi asibiti."
Ya bada sunayen wadanda suka rasu kamar haka; Nasiru Umar, 30; Abdulkadir Nura, 25; Dahawi Garin-Babale 35; Hamza Adamu, 15; Sulaiman Garin-Babale, 35; Idris Adamu, 40; da Salisu Garin-Babale, 40.
Asali: Legit.ng