Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari

  • Bayan shekaru biyu tsare a gidan yari, kotu ta yanke hukunci kan matashi dan jihar Kano, Mubarak Bala
  • Mubarak Bala ya amsa jerin laifukan da ake zarginsa da su na batanci ga addinin Musulunci kuma ya bukaci Alkali ya sassauta masa
  • An tsare Mubarak Bala ne bisa kalaman da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda ya janyo cece-kuce

Kano - Kotu ta yanke hukunci kan karar da aka shigar kan Shahararren matashin da ke ikirarin bai yarda da Allah ba, dan asalin jihar Kano, Mubarak Bala, ranar Talata, 5 ga Afrilu, 2022.

Wata babban kotun jihar Kano dake zamanta a Audu Bako Secretariat ta yanke masa hukuncin daurin shekaru ashirin da hudu a gidan gyaran hali bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da su.

Kara karanta wannan

Mubarak Bala yayi watsi da lauyansa a kotu, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su

Gabanin yanke masa hukunci, Mubarak ya bukaci kotu ta sassauta masa saboda bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba don tada tarzoma.

Ya yi alkawarin cewa ba zai sake maimaita abinda yayi ba.

Alkalin kotun, Justice Lawan, ya sanar da jefasa gidan gyara hali tsawon shekaru 24, rahoton Daily Nigerian.

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari
Yanzu-yanzu: Kotu ta yankewa Mubarak Bala hukuncin shekaru 24 a gidan yari Hoto: BBC Hausa
Asali: Twitter

Sabanin da ya auku tsakanin Mubarak Bala da Lauyansa a kotu

Yayin zaman kotun, an karanto wa Mubarak Bala sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook inda yayi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

Bayan amsa duka laifukan batancin da ake tuhumarsa da shi, lauyan Mubarak, James Ibor, cikin mamaki ya bukaci kotu ta bashi daman sa labule da shi don masa bayanin abinda ka iya biyo bayan amsa laifin da yayi.

Kara karanta wannan

Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid

Bayan nuna alamun ya gamsu, Lauyan ya sanarwa Alkali cewa Mubarak Bala ya canza ra'ayinsa, yana son sauya amsar da ya bada, rahoton BBC.

Sai Alkali mai shari'a ya tambayi Mubarak shin ko haka lamarin yake, Mubarak Bala yace sam, ba zai sauya amsar da ya bada na amincewa da laifukan da ake tuhumarsa da su ba.

Bayan jaddada masa nauyi da tasirin amsa laifinsa da Alkali yayi, Mubarak yace tabbas ya fahimci komai kuma ba tursasashi akayi ba, kuma ra'ayinsa ne.

Me Mubarak Bala yayi?

A ranar 28 ga Afrilu, 2020, Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta kama Mubarak Bala bisa zarginsa da yin batanci ga addinin Islama.

An kama matashin ne bayan wata kungiyar lauyoyi ta shigar da korafi a ofishin kwamishinan 'yan sanda na Kano bisa zarginsa da cewa ya zagi annabi Muhammad a shafinsa na 'facebook'.

Korafin lauyoyin, mai dauke da sa hannun S.S Umar ya bayyana cewa, "mun kawo korafi ne a kan wani mai suna Mubarak Bala dan unguwar Karkasara a Kano.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

"An haifi Mubarak a gidan Musulunci amma saboda wasu dalilai na kashin kansa sai ya zabi ya bar addinin, ya zama marar addini, a 2014. Tun da ya bar addini ya ke wallafa sakonnin da basa yi wa Musulmai dadi a shafinsa na 'facebook'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng