Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu
- Korarren limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya sanar da cewa korarsa sadaukarwa ce da ta zama dole ya yi
- Ya sanar da cewa, ya yi hakan ne domin talakawan Najeriya da ba su da muryar da shugabanni za su ji su
- Sheikh Nuru ya ce zai fara limanci a sabon masallacin bayan kwatas din CBN daga ranar Juma'a mai zuwa
Abuja - Tsohon babban limamin masallacin Apo da ke Abuja, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce korarsa da kwamitin gudanarwa na masallacin ya yi, wata sadaukarwa ce da ya zama dole ya yi domin talakawan da ke cikin wahala da kuma fadin gaskiya ga masu mulki.
Sheikh Khalid ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard a Abuja ranar Litinin da daddare, inda ya kara da cewa korar tasa bai girgiza shi ba.
Vanguard ta ruwaito cewa, ya kara da bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na wani sabon masallacin Juma’a da ke bayan kwatas din babban bankin Najeriya (CBN), Abuja, ya nada shi ya jagoranci jama’a daga ranar Juma’a 8 ga Afrilu.
A cewarsa, “Kora ta ya bayyana yadda Najeriya take a yau. Mutane da yawa suna fakewa da addini don su aikata duk wani abu na rashin kyautatawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Irin wadannan mutanen ba za su yi wata-wata ba sai sun ga sun kawar da mutane iri na wadanda ke magana da yawun talaka kuma suke fadin gaskiya ga shugabanni a madadin 'yan Najeriya.
“Wannan shi ne sakamakon mu saboda mun daidaita da jama'a kuma muna gane wahalhalunsu.
Da izinin Allah , zan fara sabon limanci a ranar Juma'a mai zuwa, saboda a matsayinmu na malamai, muna bukatar hanyar fadakarwa.
"Akwai Masallacin Juma'a da muka gina a bayan kwatas din CBN a Abuja, yanzu ni zan dinga limanci a can."
Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi
A wani labari na daban, 'yan Najeriya sun yi martani kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid da aka yi daga limancin Masallacin Apo da ke Abuja.
Vanguard ta ruwaito cewa, an dakatar da Nura ne sakamakon caccakar shugaban kasa Muhammad Buhari da ya yi kan farmakin da aka kai wa jirgin kasan da ya debo fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da ta gabata.
Jama'a da dama sun kushe hukuncin kwamitin Masallacin yayin da wasu kuwa suka goyi bayan hukuncin, Vanguard ta ruwaito.
cin kwamitin Masallacin yayin da wasu kuwa suka goyi bayan hukuncin, Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng