Bayan harin Tsafe, jami’an tsaro sun bankado maboyar yan bindiga a Zamfara
- Rahotanni sun kawo cewa jami'an tsaro sun bankado maboyar yan bindiga a yankin Tsafe da ke jihar Zamfara
- Shugaban karamar hukumar Alhaji Aminu Mudi Tsafe, ya tabbatar da cewar sojoji sun gano mabuyar ne sakamakon bin sahun maharan da suka yi bayan wani hari da suka kai
- A ranar Lahadi da daddare ne maharan suka kai farmaki garin Tsafe, inda suka halaka mutane da dama
Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun gano wata maboyar yan bindiga da ke kai hare-hare a yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa shugaban karamar hukumar ta Tsafe, Alhaji Aminu Mudi Tsafe, shine ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu, yayin da yake zantawa da manema labarai.
Rahoton ya nakalto Mudi yana cewa:
“Yayin da yan bindigar suka kai wani farmaki a ranar Lahadi, sai dakarun sojoji suka bi sahunsu, a nan ne suka gano maboyar miyagun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Gano maboyar tasu zai taimaka mana wajen kai masu hari tare da lalata sansanin tasu, kuma tuni jami’an tsaro suka fara shirin yin gaba-da-gaba da su.”
Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane har da ɗan Kwamishinan jiha
Mun dai ji cewa wasu yan bindiga a ranar Lahadi da daddare, sun kai hari garin Tsafe, hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun halaka mutane da dama.
Mazauna garin sun bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗan da aka kashe shi ne ɗan Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Mamman Tsafe.
Sai dai har yanzun, kwamishinan da kuma gwamnatin Zamfara ba su ce uffan ba dan tabbatar da lamarin a hukumance.
Asali: Legit.ng