Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram 10 sun fito daga daji, sun mika kansu da makamansu ga sojoji
- Wasu 'yan ta'addan Boko Haram sun ajiye makamai, sun mika kansu ga jami'an sojojin Najeriya a jihar Borno
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, 'yan ta'adda 10 da iyalansu ne suka mika wuya tare da makamai ga sojin na Operation hadin kai
- Sojojin Najeriya na ci gaba da karbar tubabbun 'yan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno tun Satumban bara
Borno - Wasu ‘yan ta’adda 10 na kungiyar Boko Haram/ISWAP da ‘ya’yansu, a ranar Lahadi, sun mika wuya ga sojoji a jihar Borno, kamar yadda wata majiyar leken asiri ta bayyana, Leadership ta ruwaito.
A cewar majiyar, ‘yan ta’addan da suka mika wuya, wadanda suka hada da maza 10 da yara 5, sun fito ne daga maboyarsu da ke kusa da kauyen Jango da tsaunin Mandara a Gwoza inda suka mika wuya ga sojojin bataliya ta 151 a Banki, karamar hukumar Bama a ranar 3 ga Afrilu, 2022.
Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
An ce ‘yan ta’addan masu biyayya ne ga kungiyar Jama’tu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) ta Boko Haram na Malam Bakura Salaba, wanda Bakura Buduma, shugaban Boko Haram ya kashe kwanan nan; magajin Abubakar Shekau.
Majiyar leken asirin, Zagazola Makama a tafkin Chadi, ya kara da cewa maharan sun aje makamansu ne sakamakon ci gaba da luguden bama-bamai ta sama da kuma wani gagarumin aikin share fage da dakarun Operation Hadin Kai suka yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton tsaron ya ce, 'yan ta'addan sun mika bindigogi da wukake da kudi Naira 600,000 ga sojojin Najeriya, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.
Ya kuma kara da cewa, 'yan ta'addan da ‘yan uwansu za su samu kulawar likitoci a wata cibiyar kula da lafiya ta sojoji.
Bayan sun kammala za a dauki cikakken bayaninsu da bincike daidai da tsarin da ya dace na duniya wajen ji da irin wadannan lamari.
Ya zuwa yanzu dai akalla ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 50,000 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas tsakanin Satumba 2021 zuwa Afrilu 2022.
Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22
A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kai samame a wasu gidaje a Anguwar Maji, cikin garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu mutane 22 bayan sa’o’i 24 da ziyartar babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba.
Jere, wanda ke da iyaka da Tafa-Sabon-Wuse a Jihar Neja, na kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, inji rahoton Daily Trust.
Wani mazaunin Anguwar Maji, Shehu Bala, wanda ya tabbatar da sace mutanen a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi.
Asali: Legit.ng