Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

  • Uwargidar tsohon shugaban kasa, Maryam Abacha, ta bukaci al’umman kasar da su rungumi dabi’ar yafiya
  • Maryam wacce ta yi bikin cikarta shekaru 75 a duniya a kwanan nan ta ce ta yafewa dukkanin mutanen da suka yiwa ahlinta laifi
  • Dattijuwar ta kara da cewar Allah ya tsarkake mata zuciya sannan cewa saboda haka, tana iya mutuwa ko a yanzu ko ma a gobe

Uwargidar marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Janar Sani Abacha, Maryam Abacha, ta bayyana cewa ta yafewa duk wanda ya kuntatawa ahlinta.

A cewar wata sanarwa da iyalan tsohon shugaban kasar suka fitar, Maryam ta bayyana hakan ne a ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, yayin bikin cikarta shekaru 75 a duniya, jaridar The Sun ta rahoto.

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa
Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa Hoto: Kano focus
Asali: UGC

Nigerian Tribune ta kuma rahoto cewa uwargidar tsohon shugaban kasar ta ce a yanzu tana iya yafiya da kuma manta duk wasu radadin da ta ji saboda Allah ya tsarkake mata zuciyarta kuma don haka, a shirye take ta tunkari mutuwa a duk lokacin da ya zo.

Kara karanta wannan

'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari

Maryam Abacha ta ce:

“Ina so na yi amfani da wannan damar don sanar da dukkanin mutanen da suka hallara a nan da wadanda basa nan cewa muna ci gaba da godiya ga Allah madaukakin sarki kan duk abun da ya faru da mu imma me kyau ko mara kyau. Ina kuma so kowa ya sani cewa na yafewa wadanda suka yi mana laifi sannan ina rokon wadanda muka yiwa laifi da su yafe mana saboda Allah ya tsarkake mani zuciyata kuma har yanzu ina raye sannan ina godiya ga Allah madaukakin sarki kan haka. Ina iya mutuwa a yanzu ko a gobe, ina godiya ga Allah a iya tsawon rayuwata.
“Ga wadanda suka yi mana laifi, ina amfani da wannan damar wajen cewa na yafe masu duka. Ina fatan za mu yafi junanmu sannan Allah ya yafe mana dukka.”

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Uwargidar tsohon shugaban kasar ta yi amfani da taron wajen yiwa kasar addu’an samun zaman lafiya da hadin kai. Ta kuma yi addu’an bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasar yayin da take korafi kan matsalolin rashin tsaro da suka yiwa kasar katutu.

Ta yi kira ga shugabanni da al’umman kasar da su ji tsoron Allah a harkokinsu.

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

A wani labarin, iyalan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha ta bakin lauyansu na Durbar Hotel Plc, Kaduna, Dr Reuben Atabo, SAN, suna neman a biya su diyyar N11,509,399,355.44 kan rushe hotel dinsu da gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi a Janairun 2020.

Cikin karar da iyalan na Abacha suka shigar mai kwanan watan 10 ga watan Maris din 2022, a babban kotun jihar, sun kuma nemi a biya su N200 miliyan saboda musu kutse a gida/fili, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah da amsa-kuwwa

Dr Atabo ya bukaci babban kotun jihar da Mai shari'a Hannatu Balogun ke jagoranta ta dakatar da duk wasu matakai da wanda aka yi karar suka dauka kawo yanzu da ya danganci gininsu da ke Lamba 1 Independence Way Kaduna na mika shi ga wani daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng